✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubu karamin laujen silin madambaci (1)

Duga-dugin dogewa Dagirgirin dagewa Dogarin dakatarwa damarar daurawa daurin butar malam ba walawa Dubu karamin laujen silin madambaci Dumbuji dambun nama ka ci Dambarwar kacici-kacici…

Duga-dugin dogewa

Dagirgirin dagewa

Dogarin dakatarwa

damarar daurawa

daurin butar malam ba walawa

Dubu karamin laujen silin madambaci

Dumbuji dambun nama ka ci

Dambarwar kacici-kacici

Dubbai na ta laluben kalaci

Dafdalar dillalan dolanci

An san masu kulla munafunci

Makirai masu makirci

Da suka jefa jama’a a kunci

Dabarbarun dabbanci

Kasuwancin kaso-kason wawanci

Masu fuka-fukin fatauci

Sun fatattakin talauci

Wasu na sana’ar dukanci

Jimar fata na kawar da kaskanci

A zaburi aura ban da sokwanci

Shan sholishon shashanci

Tabar harawa na sa ai sakarci

Hodar ibilis jigon ibilisanci

Shaye-shaye da romon iskanci

kwayoyin mamaye kwanyar lalaci

A dai kiyayi tumasanci

Ai fafutikar kwatar ’yanci

Ban da tabarar dabbanci

Ko waskiyar wawanci

Tunkurar takurar Turanci

Bankar hayakin buki

Sai kauran karyar yaki

Ya kakaba tagiyar saki

In aka ce ya ja baki

Sai ya ce haruffa sun yi baki-baki

Dubu karamin laujen silin tukunyar dambu

karma-karma an garkameta da gambu

Mu yunkura da aikin lambu

’Yan dugwi-dugwi ai musu bambu

An dabbaka aiki marar aibu

Lallai kada ai kasala

bata-gari sun sa an hassala

Domin sun yada badala

Sun fetsare da tsallen tsula

Sun jefa jama’a a wahala

Amalala

Ya tsula

Ya kuma tsulawa da ya lula

Kayan dauda a jefa gassala

Harhado da atamfar kamfala

A wannan sabuwar shekara

Mu saurari carar zakara

Kar ai mana kakara

Matsaloli za su daina faskara

A shawo kan masu kangara

Tuni nasan an kagara

Aika-aika na da matukar gundura

Sai a daura damara

Matsaloli su sha makara

kalubale ya zam abin tunkara

A dadddage

A dadddage

barna ta rududdge

Artabun bera da mage

Laulayin hankaka da jemage

Siyasa ana ta kada mata kuge

Wasu na ta shirin yin kage

Don su samu dage-dage

Har su hada da dabge

Jar miya ta fi gaban jajjage

A dai kiyayi masu kwange

Miyagu gwanayen coge

Mai ramar keta lange-lange

Sai a hada shi da sangeJante na yi wa uwar jiki zabge

Masu sake-sake

Da ke leke-leke

A daina feleke

A fito keke-da-keke

A fahimci farfaru da bakake

Gambar wastsattsake na feke

An yi wa juhala kisan mummuke

Adala ta cafke damke

An fasko masu wasa wukake

Fito na kango a make

Jita-jita babu tushe

Asusu ne an wawushe

kiren kanzon kuregen shan taushe

Farautar daji sai Baushe

Rike hawansa Hausar Bahaushe

Barankadamar bargar bisashe

Ta karade kowane sashe

Tsofaffi na taunar daushe

Duk hakora sun dusashe

Wawulo na da magogin murmushe

Zancen marasa kishi ya zam yasashe

Yadda sukai mana kwashe-kwashe

Sun yi nashe-nashe

Sun bar wasu na ta lashe-lashe

karyar karau ta farfashe

Masu hassada da kushe

Da suka sa muna ta a she-a she

Su ke yi wa kasarmu cushe

batan-bakatantan ya sa sun cunkushe

Domin an hasko su gari ya washe

Mu farmaki masu bunburutu

Cinikin mai suka yi wa buruntu

Ana ta yi musu surutu

Batutuwa har a cikin kurtu

Matsalar mai ta sa wasu sun zautu

Halin-burtu

A badda kama ai barna

Zakin zagon kasa sun dana

Baba ya ce ya hana

Sunkurun sagaraftu

Baba yai nadin matattu

An ga kuskure rututu

Na tabbata babu ganganci

An dai so yin wulakanci

An faskomasu kulla kutu-kutu

Ana ta ’yan gyare-gyare

Cike gurbi da wadanda ke raye

An rairaye

Tun daga rana zuwa dare

Kowane tudu da gangare

An kankare

An yi zare-zare

Babu sare-sare

Kowace badakala an warware

An karkare

Dajine damben kutare

Na ga ziryar kadangare

Yai kai-kawo kan kututture

Da tsakar rana ya jure

Har sai da aka karkare

Gayu sun gantsare

Fitinannu sun fetsare

Fandararru sun fandare

Tambadaddu sun tubure

batattu sun botsare

Masu rudani

Cutarku ba ta da magani

Kallon da kuke yi wa shugabanni

Jama’a na yi muku gani-gani

Suka da burtsatsen raunin tunani

Baban-burin-huriyya

Ka damke masu kamuya-muya

kara kaimin aiki a Haurobiya

A yi wa al’umma tarbiyya

Tarairaya na sa ai biyayya

Tsintsiya madaurinki guda

Hada karfin sharar jibar dudduga

Dole sai an ja daga

A daina ganda

kwazon aiki muka gada

An yi karaf-kakkaf

An shammaci masu kwashi kwaraf

Da suka yi wa lalita karkaf

Abn damke su caraf

A kara tsayuwar tsanaki tsaf

Baba saura ’yan zungura

Da suka tursasa rayuwar takura

Al’umma ta sha makura

Tabargazarsu ta ci tura

Lallai a hana su takun bankaura

Matsalar Baban Carin-ciri

Ciyawa yai wa ciron iri

Dukiya yai mata cin birbiri

Na-mujiya aka kura masa kuri

Mahukunta a sa shi a mari

Ta’asar inshora

Uwar jiki al’umma na da shawara

Sharbar shawarmar shirwa shiru

Minista ya ci shiru

Bokan Turai kar ai maka kakara

Kasuwar jaririn jari

Inda ake jalauta jari

Tabargazartunkuzar wando

An jefa ta an Kwando

Binm bahasi kar a bari

Uwargidan asusu

Kinkimi-Adadun Asusu

Kar ki taima wa aikin kusu

Don an yi kurmusu

Kar ai taron shasha da sususu

A duba batun Gwarzon gwaraza

Kurarsa tai gaza

Ya tunkari karzaza

Mai borin barhaza

Da yai ta’asar banza

A fallen sabon babi

Kowane shafi a bi

Ai ta karatun adabi

Daga gobe zuwa jibi

Kyawawan ta’adun su rike kanbi

Al’umma da tai juriya

Dogewar dauriya

Sai tai murmushi da dariya

Himma dai mutan Haurrobiya

Lallai kar mu yarda da wariya

babatun baudiyya

buruntun barauniya

Sakarcin sukuwar godiya

dumamar yanayin dirkaniya

Rukukin rarakar rafkiya