✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Don taya Fintiri murnar cin zabe muke tattaki daga Kaduna zuwa Yola’

Wadansu matasa uku masu suna Dayyabu Zakariya mai shekara 37 dan Unguwar Tudun Wada a Kaduna da Hayatu Nuhu mai shekara 25 dan Karamar Hukumar…

Wadansu matasa uku masu suna Dayyabu Zakariya mai shekara 37 dan Unguwar Tudun Wada a Kaduna da Hayatu Nuhu mai shekara 25 dan Karamar Hukumar Soba da Abdul’aziz Jafar mai shekara 23  daga Tudun Wada, Kaduna suna yin tattaki daga Kaduna zuwa Yola don taya zababben Gwamnan Jihar Adamawa Alhaji Umaru Fintiri murnar cin zabensa.

Da yake zantawa da Aminiya a lokacin da suka isa Gombe, Dayyabu Zakariyya ya ce sun taso ne daga Jihar Kaduna saboda haushin faduwar dan takarar Gwamnansu na PDP a jihar Alhaji Isa Ashiru, Fintiri kuma ya ci zabe a Adamawa shi ne za su je su taya shi murna.

Ya ce tun ranar Juma’a 12 ga  Afrilu suka taso daga Kaduna, a kwana na bakwai suka isa Gombe kuma ya ce ba su hadu da matsaloli a hanya ba sai dai abokin tafiyarsu daya ya da ya yi jinya, inda suka jira har ya samu sauki a garin Saminaka sannan suka ci gaba da tafiya.

Dayyabu Zakariyya ya kara da cewa duk da suna buga kwallon kafa a wannan tattaki kafafunsu sun kumbura amma abin ya zo musu da sauki.

A cewarsa, a kullum idan suka yi tafiya ta sa’a hudu ko biyar sai su huta inda suke tafiya ta sa’a 14 a wuni suna kuma fara tafiyar ce daga karfe 6 na safe zuwa karfe 8 na dare sai su kwanta su huta.

“Idan dare ya yi mana muna kwana a masallacin kauye ko gari amma idan muka isa gari inda ’yan PDP suna ba mu wajen kwana,’ inji Dayyabu.

Ya ce, “Tunda muka fito ba mu kyauta a hanya ba da guzurinmu muka taho amma a nan Gombe komai ya kare mana sai dai da yake mun dau niyya ba za mu karaya ba saboda kamar a nan Gombe mun samu wanda aka hada mu da shi ya saya mana abinci.”

Ya ce wanda suke tattakin dominsa Umaru Fintiri ya san suna zuwa kuma idan suka je za su ba shi shawarwarin biyan albashi a kan lokaci da biyan ’yan fansho sannan ya kyautata rayuwar al’ummar Jihar Adamawa.

Daga nan sai ya shawarci ’ya’yan Jam’iyyar PDP su rika kula da mutuncin mutane sannan Fintiri ya kula da sha’anin tsaro.