✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Don hada kan matasan Kudancin Kaduna muke shirya wasanni – Alake Ahmadu

Kodinetan kungiyar da ke shirya wasan kwallon kafa a Kudancin Kaduna, ‘Southern Kaduna Soccer Promoters (SOKASOP), Ibrahim Ahmadu (Alake) ya bayyana cewa suna shirya irin…

Kodinetan kungiyar da ke shirya wasan kwallon kafa a Kudancin Kaduna, ‘Southern Kaduna Soccer Promoters (SOKASOP), Ibrahim Ahmadu (Alake) ya bayyana cewa suna shirya irin wadannan wasanni ne don samar da hadin kai a tsakanin matasan da ke yankin da kuma kokarin zakulo zakakarun matasan da ke taka leda wanda zuwa yanzu sun yi nasarar zakulo ‘yan wasa daga yankin da ke buga wasan firimiya ta kasa da kuma wadanda suka fita kasashen waje.
Shugaban, ya yi wannan furuci ne a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya a karshen makon jiya.  Ya ce baya ga samar da zaman lafiya da wasan kan haifar, yana kuma samarwa matasa aikin yi domin wasu ta hanyar da suke cin abinci kenan.
Alake Ahmadu, ya bayyana cewa a yanzu haka akwai wasannin karshe uku da suka rage (Finals) na kofunan wasu fitattu da ake bugawa, kamar kofin Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-rufa’I, wanda kungiyoyin kwallon kafa na Malam Tagwai Sambo FC dake Moroa a karamar Hukumar kaura, wacce za ta kara da takwararta ta Garaje Bombers FC dake garin Kafanchan a karamar Hukumar Jama’a. Sai wasa na biyu da kungiyar kwallon kafa ta Unguwar Nungu Selected FC dake karamar Hukumar Sanga za ta fafata a wasan karshe (final) da Jama’a Emirate FC na garin Kafanchan a gasar cin kofin Manjo Hamza Al-Mustafa. Wasa na uku kuwa wanda shi ma na karshe ne, za a kara ne tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Damakasuwa United daga karamar Hukumar Kauru da kuma takwararta, Tum United dake karamar Hukumar kaura a wasan karshe na cin kofin Sanata mai wakiltar Kudancin  Kaduna, Sanata danjuma La’ah (Shettiman Kagoro).