Gwamnoni da Ministoci da sauran kusoshin jam’iyyar APC da suka fito daga yankin Arewa maso Yammacin Najeriya sun ce dole dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Bola Ahmed Tinubu ya dauki Mataimakinsa a takara daga yankin.
Bukatar hakan ta biyo bayan wani taro da suka yi ranar Alhamis a Abuja, don tattauna batun makomar Mataimakin dan takarar.
- An yi bikin rada wa Amurkawa 40 sunayen gargajiyar Ibo a Enugu
- Falala 10 ta kwana 10 na farkon Zul-Hijjah
Masu ruwa da tsakin sun bigi kirjin cewa yankinsu ya fi kowanne samar da ruwan kuri’u ga jam’iyyar APC mai mulki a zabukan 2015 da 2019.
Jihohin da ke yankin dai sun hada da Sakkwato da Kebbi da Zamfara da Jigawa da Kaduna da Kano da Katsina, kuma nan ne yankin da Shugaba mai ci, Muhammadu Buhari ya fito.
Yayin da rage kusan wata biyu a fara yakin neman zaben babban zaben 2023, har yanzu Bola Tinubu dai ya ce yana laluben wanda zai yi masa Mataimaki.
Sai dai a cikin takardar bayan taron da suka fitar mai dauke da sa hannun Mataimakin Shugaban jam’iyyar na kasa na shiyyar, Salihu Mohammed Lukman, ya ce taron ya sami halartar Gwamnoni masu ci da ’yan takarar Gwamna da kuma Mininstoci.
Takardar ta ce, “taron na jinjina wa zabukan fitar da gwani a matakan kasa da jihohi, sannan ya tattauna kalubalen da ke fuskantar jam’iyyar a jihohi da hanyoyin da za a bi wajen magance su cikin gaggawa.
“Taron ya duba gudunmawar da yankin Arewa maso Yamma yake bayarwa ga ci gaba da kuma nasarar APC, wanda ya samar da kaso 39 cikin 100 na kuri’un da APC ta samu a zabukan 2015 da 2019.
“Saboda haka, mun yanke shawarar hada karfi da karfe wajen hada kai da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar,” inji takardar bayan taron.