✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar Haramta Bara a Kano: Za a fara kama iyayen yara

Gwamnatin jihar Kano ta haramta bara a titunan jihar. Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin bikin mika takardun daukar…

Gwamnatin jihar Kano ta haramta bara a titunan jihar. Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin bikin mika takardun daukar aikin malanta ga mutane 7,500 a birnin Kano.

Gwamna Ganduje, ya ce gwamnati ta dauki wannan matakin ne domin tabbatar da tsarinta na ba da ilimi kyauta kuma dole ga ‘yan firamare da Sakandare na fadin jihar su amfana da sabon tsarin da aka kaddamar.

Ganduje, ya ce daga yanzu dole ne makarantun allo su shigar da darussan turanci da lissafi cikin tsarin koyarwarsu.

“Duk malamin almajiran da bai amince da wannan doka ta gwamnatin ba, ya tattara ya fice daga jihar Kano.”

Duk almajirin da aka kama yana bara, to ba almajirin za a kama ba, za a je a taso keyar mahaifinsa ko kuma wanda yake zama wurinsa zuwa kotu domin a hukunta su.