Gwamnan Jihar Delta Dokta Ifeanyi Okowa ya sa hannu a kan dokar hana kiwon shanu a fadin jihar.
Dokar wadda Majalisar Dokokin Jihar ta mika wa Gwamnan an fara muhawara a kanta ne tun wata uku da suka gabata.
Tun farko Gwamnatin Jihar ta ce za ta kafa kwamitin kula da dokar hana kiwon wanda zai kunshi Fulani makiyaya lamarin da Fulanin suka tubure.
Hakan na zuwa ne bayan kafa dokar a Jihar Benuwai da wasu jihohin Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas, dokar da Fulani makiyaya ke cewa, ba ta haifar musu da mai ido ba sai haddasa mummunar gaba da kiyayya da auka wa juna da hare-hare.
Gwamnatin Jihar Delta, ta ce a karkashin dokar duk saniyar da aka kama tana kiwo za a ci tararta Naira dubu 100 yayin da makiyayin za a ci tararsa Naira dubu 500.
Sai dai makiyayan da suke ganin an kafa dokar ce domin kuntata musu sun shaida wa Aminiya cewa, hakan zai haifar da kiyayya da gaba da fada a tsakaninsu da ’yan asalin jihar lura da cewa suna zaune lamilafiya da ’yan asalin jihar da kuma gwamnati.
Idan za a iya tunawa an sha samun rashin jituwa a tsakanin Fulani makiyaya da ’yan asalin jihohin Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma da manoma a wuraren da aka kafa irin wannan doka.
Mai magana da yawun Kungiyar Fulani makiyaya mazauna Jihar Delta, Barista Idris Abubakar ya ce, “Gaskiya tarar Naira dubu 500 a kan kowane Bafulatanin da aka kama yana kiwon sa ko saniyarsa kuma kowace daya zai biya tarar Naira dubu 100, abu ne da ba za mu amince da shi ba.
Mu ma ’yan Najeriya ne kuma muna zaune ne a jihar nan sama da shekara 50 wadansu daga cikinmu ma a nan aka haife su, a nan muka tashi, nan muka yi karatu alhali yawancin Fulani nan mazauna jihohin Arewa ne mu kuma mazauna nan ne tafiya za su yi su bar mu da dokar a kanmu,” inji shi.
Barista Abubakar ya ci gaba da cewa, “Girman matsalar ita ce za ta haifar da kazamin rikici a tsakanin mu Fulani da al’ummar jihar da ma gwamnati, domin fada na iya barkewa a tsakanin Bafulatani da wanda ya ce, zai kashe masa saniya ko kwace masa dabba.
“Irin wannan fada ya faru a wasu jihohi da aka kafa doka irin wannan, babu yadda za a yi a ce a kwace wa Bafulatani saniya a zauna da shi lafiya. A nan aka haife mu, nan muka tashi, nan muka yi karatu don haka gwamnati ta sake tunani kan wannan doka.”
Aminiya ta ji ta bakin lauyan Kungiyar Fulani Makiyaya Mazauna Jihar Delta, Barista Bala Mukhtar Muhammad kan ko me Tsarin Mulkin Kasa ya ce, game da daukar mataki irin wannan na hana kiwon shanu da gwamnoni ke yi?
Sai ya ce, “To gaskiya kamata ya yi a ce Gwamnatin Jihar Delta ta a je wannan doka a gefe domin a wasu jihohin an yi irin wannan doka abin bai zo da kyau ba. Tsarin Mulkin Najeriya ya bai wa kowane dan kasa damar ya zauna a duk inda yake so, kuma ya gudanar da harkokinsa na rayuwa da kasuwanci ba tare da wata tsangwama ba.”