✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar hana fita: Birnin Maiduguri ya dau harama

A Maiduguri, babban birnin jihar Borno, tituna da wuraren hadahada, musamman kasuwanni, sun cika da jama’a. A kasuwar Gamboru da ke cikin birnin, misali, an…

A Maiduguri, babban birnin jihar Borno, tituna da wuraren hadahada, musamman kasuwanni, sun cika da jama’a.

A kasuwar Gamboru da ke cikin birnin, misali, an samu cikar da ba a saba ganin irinta ba yayin da mutane ke yunkurin sayen nama da kayan miya.

Hakan na faruwa ne dai saboda mutane na ta azamar sayen abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum kafin dokar da gwamnati ta ayyana ta hana fita ta fara aiki.

Jiya ne dai a wani jawabi da ya yi ga al’ummar jihar ta Borno, Gwamna Babagana Umara Zulum ya sanar da dokar ta hana fita.

“Bisa ikon da doka ta ba ni, na rattaba hannu a kan cewa cutar coronavirus babban bala’i ce, don haka ina sanar da cewa hana duk wata zirga-zirga a duk fadin wannan jiha, kama daga karfe 10:30 na daren Laraba, har zuwa mako biyu.

“Don haka ina kira ga dukkan jama’ar jihar Borno da su kasance a gidajensu, a rufe duk wuraren kasuwanci, sannan an haramta duk wani taro.

“Tuni an umarci jami’an tsaro da su sanya ido a kan tabbatar da wannan umarni.

“Bugu da kari, gwamnati za ta yi amfani da wannan lokaci wajen kara kaimi don ganin an tantance duk wanda ya yi mu’amala da wanda ya kawo cutar jihar Borno”, a cewar Gwamna Zulum.

Gwamnan ya kuma yi alkawarin kafa kwamitin da zai binciko yadda aka shigo da cutar, yana cewa an umarci Kwamitin Cika Aiki Kan Yaki da Coronavirus a karkashin jagorancin Mataimakin Gwamna Umar Usman Kadafur ya rinka sanar da jama’a halin da ake ciki game da samun abinci, magunguna da kuma harkar banki.

“Kowa ya san halin da jihar Borno ta tsinci kanta a ciki, a tsawon shekaru 11 tana fama da Boko Haram, ga kalubalen da ’yan gudun hijira suke fama da shi…

“Dole za a ci gaba da tallafa musu, haka mutane masu karamin karfi su ma za a san yadda za a rinka tallafa musu”, inji shi.

Daga sai Gwamna Zulum ya bukaci al’umma su yawaita addu’ar Allah Ya kawo dauki a kan wannan cuta.

Aminiya ta jiyo ta bakin wasu mazauna birnin na Maiduguri a kan wannan lamari.

A cewra Alhassan Kawu, hakika daukar wannan mataki na hana fita ya dace, duba da yadda cutar take saurin yaduwa.

“Amma dai ganin yanayin da jihar Borno ta kasance a ciki to kamata ya yi gwamnati ta samar da abinci ga al’umma domin kusan kashi 80 cikin 100 ba su da abinci sai mutum ya fita nema”. Inji shi

Ita kuwa Ba’ana Ali Kura kira ta yi ga al’umma da su kasance masu bin doka, sai dai ta bukaci gwamnati ta hannu Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) ta samar da abinci ga al’umma, don rage wahalar da jama’a suka tsinci kansu a ciki.