✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar Hana Babur: Nakasassu sun yi sallar Juma’a a harabar Majalisar Legas

Nakasassu a Legas sun gudanar da sallar juma’arsu a gaban harabar zauren Majalisar dokokin jihar Legas, a inda suka je da sanyin safiyar ranar Juma’a…

Nakasassu a Legas sun gudanar da sallar juma’arsu a gaban harabar zauren Majalisar dokokin jihar Legas, a inda suka je da sanyin safiyar ranar Juma’a domin kai kokensu bisa dokar hana tukin babur mai kafa uku a wasu sassan jihar.

Nakasassun sun ce tukin babur din shi ne kadai sana’ar da suka iya sai kuma bara, dan haka basa fatan su koma sana’ar bara kuma suma suna da iyali da suke daukar dawainiyarsu tamkar kowa.

Sun yi shirin zaman dirshan a harabar zauren Majalisar har sai an amsa masu bukatunsu, inda suka yi sallar juma’a suka kuma gudanar da addu’o’i.

Sai dai, kakakin majalisar Honurabul Mudashiru Obasa, ya lallabe su inda ya nemi su koma gidajen su domin majalisar zata duba koken nasu.

Honurabul Obasa, wanda ya sami wakilin Dan majalisa mai wakiltar Karamar hukumar Alimosho, Honurabul Bisi Yusuf ya yaba da yadda nakasassun suka gudanar da zanga-zangar cikin lumana, ya ce da zarar ‘yan majalisar sun dawo daga hutu zasu duba lamarin.

“Na yaba da yadda kuka shirya kanku cikin tsari baku tada tarzoma ba, kuka tunkare mu domin a share maku hawaye, da zarar mun kammala hutu zamu zauna mu duba koken ku, kada ku yarda bata gari suyi amfani daku wajen tada tarzoma, ku ci gaba da bin tsari kamar yadda kuka faro.” in ji shi.

Kwamrade Muhammadu Zannah, wanda ya jagoranci nakasassun ya gabatarwa ‘yan majalisar koken nasu, ya so ya nuna tirjiya inda ya nemi ‘yan majalisar su yanke hutun da suke, su zo zauren su saurare su, ya ce suma suna da iyali tamkar kowa an hana su bara kuma an hana su sana’a me ake so su ci da su da iyalansu?

Wasu daga cikin Nakasassun lokacin da suke yin Sallah

‘Yan majalisan sun lallabesu suka basu tabbacin yin zama domin duba korafin su.