✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar Hana Acaba a Legas: ‘Yan acaba na kaura zuwa Arewa

Daruruwan ‘yan acaba dauke da baburan su cikin manyan motocin tirela ne suke kan yin kaura daga Legas zuwa Arewacin kasar nan bayan da dokar…

Daruruwan ‘yan acaba dauke da baburan su cikin manyan motocin tirela ne suke kan yin kaura daga Legas zuwa Arewacin kasar nan bayan da dokar hana tukin babur a kanana hukumomin 15 na Legas da manyan hanyoyin da saman gadoji ta fara aiki a yau Asabar.

‘Yan acabar mafi aka sarin su matasa ne, sun yi cincirundo dauke da ‘yan kayayyakinsu da baburansu a tashar manyan motoci ta Ogere da ke kan hanyar Legas daga Ibadan a jihar Ogun.

Da dama na ‘yan acaba a Legas matasa ne ‘yan Arewa mafi akasarin su daga jihohin da ke fama da rikicin Boko Haram da suka hadar da Borno da Yobe da Adamawa, yawancin matasan da suka yo kaura daga wannan yanki a sakamakon rikicin Boko Haram, suna sana’ar tukin babur na acaba da babur mai kafa uku a cikin garin Legas wuraren da suka hadar da: Ikeja, Apapa, Obalende da Ikoyi inda dokar ta fara aiki.

‘Yan acaba na shirin barin Legas zuwa Arewa

Kwamrade Ya’u Musa Saka, shugaban kungiyar matasan Arewa a jihohin Yamma ya shaidawa Aminiya cewa, dubban matasan Arewa zasu sami kansu cikin matsalar rashin aikin yi biyo bayan kaddamar da dokar, dan haka ya shawara ce su da in sun koma Arewa su nemi sana’a, su shiga aikin noma da kasuwanci, “Domin gwamnatin Legas da gaske take, da idona na gani sun kawo manyan motoci masu injin markade babur, an jibge su a Apapa, da an kama babur sai ka ga an jefa cikin injin kan kace kwabo ya markade  shi, ko minti biyu ba a yi injin ke markade babur.”

Haka zalika, Kabiru Yusuf mazaunin Legas a idi-Araba ya shaidawa Aminiya cewa, yau garin Legas babu babur tamkar an kore su, ya ce an sami karancin ababen hawa, “A lunguna kadai kake ganin babura, bayan da babur ya sauke ni daga lungun na shiga sahun masu neman motocin haya wadanda a yau suka yi karanci, mun sha wuya kafin musami motar haya saboda jama’a sun masu yawa.” In ji shi.

Gwamnatin Legas ta sanar da cewa, zata samar da kananan motoci da zasu dinga jigilar jama’a a wuraren da ta haramta hawan babur.