✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dokar hana acaba a Legas: Tarzoma ta barke tsakanin ‘Yan Acaba da ‘Yan Sanda

An samu hatsaniya a tsakanin wasu masu tukin baburan acaba da keke Napep da jami’an ‘yan sanda a yankin Ijora da ke daura da Apapa…

An samu hatsaniya a tsakanin wasu masu tukin baburan acaba da keke Napep da jami’an ‘yan sanda a yankin Ijora da ke daura da Apapa a Legas.

Tarzomar ta biyo bayan zanga-zanga da ‘yan acabar suka yi ne domin nuna rashin jin dadin su da dokar hana su aiki a kananan hukumomi 15 da manyan tituna da saman gadoji a jihar.

Majiyar mu ta shaida cewa, da sanyin safiyar yau Litinin masu zanga-zanga suka rufe hanyoyi da tayoyi motoci wadanda suka kunna masu wuta, lamarin da ya sanya ‘yan sanda suka farmasu a kokarin su na hana su.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a Legas DSP Bala Elkana, ya fitar ya shaida cewa rundunar ta kame babur guda 188 da keke Napep 78 da wasu mutum da suka karya dokar su 40, ya ce rundunar ta shirya tsaf domin ganin ana bin dokar sau da kafa.