Shugaban Majalisar Wakilai Honorabul Yakubu Dogara ya bayyana kafa wata kungiyar kwallaon kafa da zai dauki nauyinta a kokarinsa na inganta harkokin wasanni a Jihar Bauchi tare da karfafa hazakar matasa a fagen kwallon kafa.
Shugaban Majalisar ya bayyana haka ne a wajen wasan karshe na cin Kofin Hadin-kai na Dogara.
(Dogara Unity Cup) da aka gudanar a karamar Hukumar bogoro da ke Jihar Bauchi.
kungiyoyin kananan hukumomi bakwai da suka fito daga mazabar Sanatan Bauchi ta Kudu inda ya fito ne suka fafata a gasar, inda kungiyar kwallon kafa ta Spiders daga Dass ta zo ta biyu, sai 3c daga Bauchi ta lashe gasar. kungiyoyin da suka zo na daya zuwa na hudu sun samu kyautar kudi da suka kama daga Naira dubu 750 zuwa Naira dubu 150.
Da yake jawabi a wajen rufe gasar, Shugaban Majalisar Wakilan ya ce bay a jin dadin yadda babu dan Jihar Bauchi a kungiyar kwallon kafa ta kasa a yanzu, inda y ace daga shekarar daga bana, zai fara daukar nauyin wata gasar kwallon kafa da za ta kunshi dukan kananan hukumomi 20 na Jihar Bauchi domina dada zakulo masu hazaka.
Ya kara da cewa zai gayyaci jami’ai daga Hukumar kwallon kafa ta Najeriya da masu gudanar da gasar cikin gida su turo jami’ansu su halarci gasar daga matakin kwata-fainal ta yadda za su iya zakulo ’yan wasan da suka fi hazaka daga kungiyoyinsu.
Ya ce, wannan hanya za ta fito da Jihar Bauchi a fagen kwallon kafa a kasar nan ta bunkasa tare da tallata ’ya’yanta a matakin duniya.
Daga nan sai Dogara ya bayar da sanarwar kafa kungiyar kwallon kafa ta sa wadda za a dauko ’yan wasanta daga kungiyoyin da suka fafata a gasar ta cin kofin Dogara Unity Cup.