Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, ya bukaci hukumomin tsaro su dauki alhakin gazawarsu wajen hana sace ’yan matan 110, inda ya ce ba za a lamunci dora wa juna laifi a tsakanin sojoji da ’yan sanda ba.
Sanarwar da Kakakin Turaki A. Hassan ya aiko wa Aminiya a ranar Talata, ta ruwaito Honorabul Dogara yana cewa, maimakon dora wa juna laifi, wajibi ne dukan hukumomin tsaro su hada hannu tare da zage dantse wajen ceto ’yan matan.
“Bayanan da aka jingina ga sojoji da ’yan sanda inda suke kokarin wanke kawunansu daga gazawa a abin takaici da abin kunya na sace ’yan mata daga makaranta a Dapchi a Jihar Yobe, babban abin Allah wadai ne. Ba za a lamunci wannan ba, kuma Majalisar Wakilai da ’yan Najeriya za su dora wa dukan hukumomin tsaron laifin gazawa. Tilas ne su dauki alhakin wannan abin takaici. Abin takaicin nan na sace ’yan matan Chibok da har yanzu ke cikin zukatanmu ya kamata ya zamo gargadi ga hukumomin tsaro su rika samar da cikakken tsaro da kare dukan makarantun da ke Arewa maso Gabas,” inji Dogara sai ya jajanta wa iyayen ’yan matan da aka sace da daukacin mutanen Dapchi, tare da yin kira ga ’yan Najeriya da masu yi mata fatan alheri su dukufa wajen yin addu’o’in dawowar ’yan matan cikin koshin lafiya.