✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Direban da ya sayar da man fetur ya kona motar ya shiga hannu

An kama wani direban motar tanka bisa zargin sace man fetur lita dubu 22 mallakar kamfanin GASTAB Haulage da ya sayar a kan Naira miliyan…

An kama wani direban motar tanka bisa zargin sace man fetur lita dubu 22 mallakar kamfanin GASTAB Haulage da ya sayar a kan Naira miliyan 2 da dubu 600, kafin ya cinna wa motar wuta ta kone kurmus, inda ya yi karyar cewa hadari ne ya rutsa da shi.

Direban mai suna Akinkunmi Ahmed da Usman Kpotun wanda ake zargin ya sayi man a hannunsa a garin Bida, Jihar Neja suna tsare a hannun ’yan sanda suna ci gaba da bincike.

Da yake nuna mutanen ga ’yan jarida a Ibadan, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Oyo, Abiodun Odude ya ce su biyun, mai saye da mai sayarwa sun amsa laifin, bayan  kama su. Sai dai Usman Kpotun ya shaida wa Aminiya cewa, “Gaskiya ni na sayi wannan man fetur daga hannun wannan mutum amma ban san cewa na sata ba ne.”

Kwaminishinan ya ce an samu kananan motoci guda 2 kirar Micra da direba Akinkunmi ya saya daga cikin kudin da ya samu da nufin a yi masa tasi da su don ya rika samun kudin shiga.

Wani direban motar tanka da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, “A lokacin da mutumin ya kammala sayar da man sai ya ga alamar yaron motarsa yana so ya tona masa asiri. Hakan ne ya sa ya dauki hayar wadansu mutanai da suka rika yawon neman yaron motar domin su kashe shi amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba. A wannan lokaci ne yaron ya sulale a boye daga garin Bida ya koma Ibadan, ya sanar da ubangidansu halin da ake ciki.”

Majiyar ta ce, “Jim kadan da samun wannan labari sai ubangidan ya sanar da ’yan sanda inda suka yi dabarun kiran Akinkunmi ta  tarho don sanin halin da yake ciki. A nan ne ya shaida masu cewa ya yi hadari da motar kuma ta kone kurmus kuma yaron motar ya mutu.”

“Ba tare da bata lokaci ba sai ubangidansa ya umarci ya dawo gida. Dawowarsa gida ke da wuya sai ya fada hannun ’yan sanda wadanda suka yi masa tambayoyin da suka kai su ga gano gaskiyar al’amarin,” inji majiyar.

Aminiya ta tambayi wani malamin Musulunci Ustaz Tahir Zubairu game da yawan aukuwar irin wannan al’amari da ma’aikata suke kulla yadda za su cutar da masu gidansu a wasu lokuta ma su hallaka su. Sai malamin ya ce, “Muna iya danganta aukuwar haka a kan rashin kyakkyawar tarbiyya a tsakanin matasa masu zumudin azurcewa cikin dare daya da suke kin yarda da kaddarar Allah. Sai kuma su kansu mutanen da suka mallaki dukiya da kadarori ta haramtacciyar hanya wanda tun a nan duniya masifu daban-daban suke fadawa a kan dukiyoyinsu. Akwai kuma wadanda Allah Yake jarabtarsu da wata masifa, idan suka yi hakuri sai Allah Ya saka musu da fiye da abin da suka rasa.”