✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Diego Costa ya koma Atletico Madrid

Bayan ya kwashe shekara 3 a kulob din Chelsea na Ingila, Diego Costa ya sake komawa kulob dinsa na asali Atletico Madrid da ke Sifen…

Bayan ya kwashe shekara 3 a kulob din Chelsea na Ingila, Diego Costa ya sake komawa kulob dinsa na asali Atletico Madrid da ke Sifen a wata yarjejeniya da ya kulla da kulob din a ranar Talatar da ta gabata.

Sai dai dan kwallon ba zai fara buga wa kuob din na Atletico Madrid kwallo ba sai daga ranar 1 ga watan Janairun 2018 saboda takunkumin da Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta kakaba mata a game da laifin sayen ’yan kwallon da shekarunsu suka gaza 18 a shekarun baya.  Yanzu takunkumin zai kare ne a watan Janairun badi, da hakan zai ba kulob din damar saye ko sayar da ’yan kwallo.

Diego Costa ya raba gari ne da kulob din Chelsea na Ingila a kakar wasan da ta wuce bayan ya rika samun sabani da koci Antonio Conte, inda kocin ya nemi ya bar kulob din don ba zai yi amfani da shi a kakar wasa ta bana ba.

Hakan ta sa kulob da dama suka rika zawarcin Costa amma a karshe ya yanke shawarar komawa tsohon kulob dinsa Atletico Madrid a kan kudin da aka kiyasta sun kai Fam Miliyan 57.