Masu iya magana kance kwanci-tashi ba wuya a wurin Allah, yau ga shi shekaranjiya Laraba mulkin demokuradiyya da kasar nan ta dawo kan turbarsa a ranar 29 ga watan Mayun 1999 ya cika shekara 14, kuma hakan ne lokaci mafi tsawo da aka taba samu ana irin wannan mulki a tarihin kasar da `yancin kai, yau kusan shekaru 53.
A bisa ga al`ada, a duk lokacin da irin wannan lokaci ya zagayo, masu mulki da `yan adawa da talakawan kasa da sauran kungiyoyi masu zaman kansu da `yan jarida da masu sharhi a kan al`amuran yau da kullum, kan yi waiwaye adon tafiya a kan yadda al`amurra suka kasance a irin wadannan shekaru, wala-alla na nasara ko rashin nasara.
Mai karatu dai ya sani cewa, tun daga ranar 15 ga watan Janairun 1966 da sojoji suka fara kutso kai cikin harkokin mulkin kasar da sunan juyin mulki, sojojin sun yi ta mazari ganin sun mayar da mulkin a hannun farar hula, mulkin da a yau ake cewa shi kasashen duniya ke yayi. Ta kai matsayin da sojojin suka yi ta alkawurran mayar da mulkin hannun farar hula, amma sai ta kasance in har ma sun yin, to sai ka tarar ba da wani dogon lokaci ba, sun sake kutso kai sun kwace mulkin, bayan kuma su ya su suka rika yi wa juna juyin mulkin. Ta ma kai matsayin da suka fara yin gwajin mulki irin na ungulu da kan zabo, wato shugaba kasa na soja a sama tare da `yan majalisun dokoki na kasa, a kasa kuma gwamnonin da `yan majalisun dokoki na jihohi, amma shi din ma bai kai labari ba. Haka aka yi ta waccan sabarta-juyarta, har Allah Ya kawo 29 ga watan Mayun 1999, ga shi kuma har zuwa yau din nan cikin yardar Allah a mulkin farar hular kasar nan take.
Wasu masu nazarin harkokin yau da kullum na kasar nan kan ce kamata ya yi a kullum idan za a yi nazari a kan nasara ko rashin nasarar mulkin wannan jamhuriya, to, a rika la`akari da wannan jawabi da na yi a sama, wanda sukan ce shi ne harsashin da aka dora ginin wannan demokuradiyya, dadin-dadawa kuma wadanda suka shugabanci a mayar da mulkin suka kuma dora tsohon soja a zaman shugban kasa na farar hula, sun kuma yi haka ne da aniyar su ga ta yaya za su sake dawowa dai a kan mulkin bayan sun ajiye kaki. Bisa la`akari da haka masu irin wancan ra`ayi suke cewa sojoji sun riga sun gurbata harkokin siyasar kasar nan bisa ga dogon lokacin da suka dauka suna mulkin zuwa tsare-tsaren da suka gudanar kafin mika mulkin (kamar shirya kundin tsarin mulki da wanda suka ba mulkin), wannan ta sanya har gobe wasu ke ganin an goya wannan demokuradiyya da tsumman zane.
Abin da ya sanya duniya ta yi caa a kan sai kasashen duniya su yi mulkin demokuradiyya, bai wuce irin yadda ake wa mulkin fassara da cewa shi ne “Gwamnatin jama`a, daga jama`a kuma don jama`a”, wato ma`ana mulkin an tsara shi a kan dukkan abin da masu gudanar da shi za su gudanar, to, lallai ya kasance da amincewar jama`ar. Amma mu zuwa yanzu kowa ya san ba abin da ake tsoma jama`a cikinsa a wannan mulkin sai idan maganar zabe ta zo, ita din ma, ba a ba mutane hakikanin abin da suka zaba. Magudin da ya zama a gidan kowace jam`iyya.
Irin wanna tsari ya sanya a kasa sai abin da shugaban kasa ya ga dama a kan dukkan abin da ya sa gaba. Haka labarin yake a jihohi ga gwamnoni, inda ka yi kasa zuwa majalisun kananan hukumomi, can ma maganar ba ta canja zane ba.
kin karbar kaddara ga masu kwadayin mulki a wannan zamani shi ne, kashin bayan da ya jefa kasar nan cikin irin mawuyacin halin da take ciki na tabarbarewar matakan tsaro da suke haddasa asarar rayukan dubban al`umma, wala-alla ta rikice-rikicen kabilanci da na addini da rashin wadatattun muhimman bukatun kayayyaki more rayuwa kamar samar da ilmi da hanyoyi da wutar lantarki da ruwan sha da makamantansu da fatara da talauci da rashin ayyukan yi da kin bin doka da oda tun daga sama har kasa (rashin demokuradiyyar cikin gida da magudin zabe) da uwa uba cin hanci da rashawa wanda kasashen duniya da suka ci gaba, a kullum suke kururuwar cewa shi ne babban abin da ya fi dakushe ci gaban kasar nan, amma ba wai don kasar ba ta da arzikin da za ta kyautata rayuwar mutanenta ba.
Alal misali, kowa ya san faman da mahukunta suka sha ko suke kan sha wajen shawo kan tabarbarewar matakan tsaro tun da aka fara wannan mulkin farar hula, kamar rikice-rikicen `yan gwagwarmayar kungiyoyin OPC da na Neja-Delta da na Jama`atu Alhis Sunah Lid Da`awti Wal Jihad wato Boko Haram da fashi da makami da rikice-rikice masu kama da addini da kabilanci, da rashin kamanta gaskiya da adalci a cikin mulki, wanda kusan shi ne ummalhaba`isin wadannan matsaloli.
Idan ka dawo a kan rashin gudanar da zabubbuka cikin gaskiya da adalci da ma karbar sakamakon zabubbukan bisa ga yarda da kaddara. A baya-bayannan dubi zaben da kungiyar Gwamnonin kasar nan suka gudanar a ranar Juma`ar da ta gabata, inda aka sake zaben gwamnan Jihar Ribas Cif Rotimi Amaechi, da irin yadda yanzu wasu gwamnoni suka kekasa kasa suka ce sam allanbaran ba su amince da zabensa ba, su Gwamnan Jihar Filato Mista Dabid Jang suka zaba, ya nuna maka irin yadda ba wanda yake shirya da ya karbi kaddara.
Duk da irin wannan tabargaza da ake fama da ita a mulkin farar hular na shekaru 14, ya zama wajibi mu yi godiya ga Allah SWT da yake mana jagora a kan yadda kasar nan take hade da yadda sojoji suka kawar da kai ba su fado fagen ba, suka mayar da tafiyar baya ba. Allah Ya ba mu shugabanni nagari a shekaru masu zuwa da za su gyara wadannan abubuwa. Barkanmu da zagayowar Ranar Demokuradiyya