A yayin da aka samu rahoton sake bullar Foliyo a Jihar Borno a makon jiya, ta tabbata cewa Najeriya ta sake fadawa cikin jerin gwanon kasashen duniya masu matsalar cutar, inda ke nan lasisin da aka ba ta na wanke ta daga cutar ya zama sokakke ke nan. Rabon Najeriya da Foliyo dai tun watan Yulin 2014.
A yanzu ke nan, daga Najeriya sai Pakistan da Afghanistan ne kadai kasashen da ke da Foliyo a duniya. Hakan na nufin cewa, sai an tsumayi har zuwa tsakiyar shekarar 2019, kafin a maido wa Najeriya takardar shaidarta, in har ba a sake samun bullar cutar a kasar ba.
Ita dai Foliyo ana daukar ta ne daga wata kwayar cuta, wacce ke addabar sassan jijiyoyin dan Adam, inda take haddasa shanyewar sassa ko dukan gabobin jiki cikin sa’o’i kadan. Haka kuma, cutar kan yadu tsakanin mutum da mutum, musamman ta hanyar gurbataccen ruwa ko abinci, kuma tana yaduwa a cikin ’yan hanji sosai. Masana sun ce, daya daga cikin mutane 200 da suka kamu da kwayar cutar kan gamu da mummunar illar shanyewar kafafuwa.
Da yake bayani game da bullar cutar, Ministan Lafiya, Farfesa Isaac Adewole ya ce gwamnati za ta yi wa yara kimanin miliyan biyar allurar riga-kafi cikin hanzari a jihohi hudu, domin dakile yaduwar cutar a matsayin matakin gaugawa. Haka kuma kimanin yara miliyan daya za a yi wa allurar a kananan hukumomi hudu na Jihar Borno, kamar kuma yadda yara da ke zaune a jihohin Yobe, Adamawa da Gombe, su ma za su samu wannan allura. Haka kuma za a ci gaba da wannan gangami a jihohi 16 na Arewacin Najeriya.
Abu ne mai muhimmanci, Ma’aikatar Lafiya ta maida hankali wajen hada gwiwa da cibiyoyin lafiya domin tabbatar da cewa an aiwatar da allurar riga-kafin a kan kari. Abin lura shi ne, akwai tababa idan Kwamitin Shugaban kasa A Kan Foliyo ya yi aikinsa yadda ya dace tun daga 2014 zuwa yanzu da aka sake samun bullar cutar.
Muna kira da babbar murya ga Gwamnatin Tarayya, da ta dauki dukkan matakan da suka dace wajen bunkasa tsaro a Arewa maso gabas, domin bayar da dama ga ma’aikatan lafiya su aiwatar da allurar riga-kafi ga yara a yankin da aka samu bullar cutar ta Foliyo. Samar da ingantaccen tsaro ga ma’aikatan zai ba su damar karade dukkan yankin, yayin gudanar da aikinsu na kakkabe cutar, sannan ya tsare su daga hare-haren ’yan ta’adda.
Haka kuma, muna roko ga gwamnati da kungiyoyin sa-kai da su yi hobbasa wajen taimaka wa yara ’yan kasa da shekara biyar da ke zaune a sansanonin ’yan gudun hijira, wajen samar masu da ingantaccen abinci. Dalili kuwa shi ne, masana sun ce ita allurar riga-kafin ba ta yin tasiri ga yaron da ke fama da yunwa ko kuma marar cikakkar lafiyar jiki. Lallai ne idan ba a yi hanzarin inganta yaran yankin da ingantaccen abinci mai gina jiki cikin lokaci ba, babu wata allurar riga-kafi da za ta yi tasiri a gare su ko an yi.
Domin dai a samu nasarar yaki da cutar nan ta Foliyo, muna kara kira ga gwamnati da ta kawo dauki ga ma’aikata da jami’an lafiya na sassan kasar nan, wajen biyansu hakkokinsu na albashi da alawus-alawus a kan kari, domin kuwa akwai daga cikinsu da suke bin bashin albashi na watanni. Idan har ba a biya su hakkokinsu ba, alhali suna kan aiki mai muhimmanci irin wannan, akwai yiwuwar a dakile himmarsu, a samu nakasu ta bangarensu.
Muna jinjina wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bayar da umurnin fitar da kudi, Naira biliyan 9.8 domin samar da alluran riga-kafin Foliyo. Haka kuma muna yaba wa Ma’aikatar Lafiya Ta Tarayya da hadin gwiwar cibiyoyin lafiya na duniya, kamar WHO, UNICEF da GPEI da suka hanzarta wajen fadakarwa da gangamin yaki da cutar Foliyo a sassa daban-daban na Najeriya da aka samu bullar cutar. Haka kuma muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hada kai da kasashe makwabta, kamar Chadi, Kamaru da Nijar, wajen wayar da kan al’ummarsu tare da yin aiki tukuru a hukumance domin yaki da cutar Foliyo.
Dawowar Foliyo a Najeriya
A yayin da aka samu rahoton sake bullar Foliyo a Jihar Borno a makon jiya, ta tabbata cewa Najeriya ta sake fadawa cikin jerin gwanon…