Tashoshin jiragen sama da dama a China sun soke tashin jirage sakamakon sake bullar cutar COVID-19 a kasar.
Jaridar Global Times ta kasar ta rawaito ranar Alhamis cewa yankin Kudancin Guangzhou da ya fi ko’ina yawan wadanda suka kamu, ya soke tashin jirage 1,000.
An kuma soke tashin karin jirage 700 a manyan tashoshin da ke Beijing.
Gwamnatin kasar ta ce ta fara aiwatra da tsauraran matakan dakile yaduwar cutar, da suka hada da soke tashin jirage, da kulle da kebewar tilas, hadi da gwajin cutar.
Duk da wadannan manufofin na kawo cikas ga tattalin arzikin China, cutar na sake mamaye kasar a baya-bayan nan.
Bayan fitar da rahoton kamuwar mutane 8,176 a ranar Laraba, hukumomi sun sake bayyana samun karin mutum 8,800 da suka harbu a ranar Alhamis.
Yankunan da aka fi samun masu cutar sun hada da manyan biranen kasar irinsu Beijing da Shanghai, da Chongqing da kuma Guangzhou.