✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Davido ya dauki nauyin karatun wani dalibi dan kasar Ghana

Tallafin ya hada da kudin makaranta da na masauki da kudin kashewa

Shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya biya wa wani dalibi dan kasar Ghana da ya gaza kammala karatu kudin makaranta har na tsawon shekara biyar.

A wani sakon da ya karade shafin sada zumunta na Twitter, an ga dalibin mai suna Morro Suleyman da ya samu makin A1 a darussa tara na jarabawar kammala sakandarensa ta WAEC a 2021, amma rashin kudi ya sanya ya gaza shiga jami’a.

A yanzu dai Davido ya bayyana ba shi kudin tallafin karatu na shekara biyar a jami’ar Adeleke da ke Najeriya, hadi da cikakken kudin masauki da na alawus din kashewa da siyan kayan karatu.

Mawakin ya ce: “Mun sami Suleyman da ke kasar Ghana, kuma mun ba shi tallafin karatu na shekaru hudu zuwa biyar, hadi da kudin masauki da na alawus a jami’ar Adeleke”.