Kungiyar Dattawan Katsina ta roki Gwamnatin Tarayya da ta kammala aikin titin Kano zuwa Katsina da aka faro tsawon lokaci.
Kungiyar ta bayyana damuwarta kan yadda ta ce aikin na tafiyar hawainiya inda aka daina aikin kusan tsawon watanni uku da suka shude kuma tuni masu aikin titin suka kwashe kayan aikinsu.
- Tarayyar Afirka ta taya Macron murnar sake lashe zaben Faransa
- Matsalar Tsaro: Birtaniya ta horas da dakaru 145 a Najeriya
Saboda haka, dattawan sun roki Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya sa baki masu aikin titin su dawo bakin aikinsu don kammala shi cikin lokaci.
Alhaji Aliyu Sani Mohammed, Sakataren kungiyar, wanda ya bayyana haka ga manema labarai a Katsina, ya ce zuwa yanzu an ci karfin aikin titin zuwa kashi 65 cikin 100.
Ya ce, “Mun damu da yadda titin Kano zuwa Katsina ya tsaya saboda mun lura ma’aikatan titin sun kwashe kayansu sun koma wani wajen ba tare da wani bayani ba.
“Ta ya za su bar irin wannan aiki mai amfani? Wannan aiki yana da matukar muhimmanci ga kasar nan, saboda Kano zuwa Katsina na daya daga cikin manyan hanyoyin zuwa Jamhuriyar Nijar.
“Saboda haka, muna rokon Minista da ya sanya baki su dawo bakin aikinsu don kammala shi. Abin da ya rage bai wuce kashi 30 zuwa 35 ba na aikin. Don haka muna roko ya dawo da su don su kammala aikin,” a cewarsa.
Idan ba a manta ba, a 2019 ne Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 29.6 don aikin fadada titin na Kano zuwa Katsina, wanda zai faro daga yankin Gidan Mutum Daya zuwa cikin garin Katsina.
Sai dai wani rahoto ya bayyana cewar an dakatar da aikin ne sakamakon gaza cika ragowar kudin kwangilar aikin da Gwamnatin Tarayya ta yi.