✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darul Rahma za ta sake aurar da zawarawa a Kaduna

kungiyar Darul Rahma ta shirya sake daura wa zawarawa aure a Jihar Kaduna nan da wani dan lokaci.Shugaban kungiyar Sheikh Is’hak Yunus Al-Madani ne ya…

kungiyar Darul Rahma ta shirya sake daura wa zawarawa aure a Jihar Kaduna nan da wani dan lokaci.
Shugaban kungiyar Sheikh Is’hak Yunus Al-Madani ne ya bayyana wa Aminiya haka ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce suna shirye-shiryen da suka dace don gudanar da bikin karo na biyu.
Ya ce: “kungiyarmu ta fara shirin kara aurar da zawarawa karo na biyu. Mun samu fiye mutum 300 da suka bayyana sha’awar shiga shirin kuma kwamitinmu na bincike da tantancewa ya yi nisa da aiki, amma ba mu sa ranar da za a yi bikin ba tukuna. Muna jira har sai sun kammala aikin tantancewar.”
Sheikh Yunus ya ce suna gudanar da wadannan ayyukan ne da kudin da kungiyar ta tara, amma gwamnatin Jihar Kaduna ba ta kai ga ba da nata taimakon ba. Ya kuma ce, sun dakatar da raba fom ga masu sha’awar shiga shirin har sai an kammala aikin tantance wadanda ke hannu.
Ya ce “kofa a bude take ga abokan zamanmu Kristoci da ke da sha’awar shiga shirin, saboda kara wanzar da fahimtar juna da hadin kai a jihar. Dalilin tashe-tashen hankulan da jihar ta yi fama da su a baya, ya sa mata da dama sun rasa mazajensu. Wannan ya sa muke ganin ya kamata a ce matan da sauran masu sha’awar shirin, koda mace bata taba yin aure ne ba, duk muna maraba da su. Addinin Kirista kansa ya aminta cewa mace na da damar kara aure, idan mijinta ya mutu. Da wannan ne muke ganin dacewar saka ’yan uwanmu Kiristoci cikin shirin.”
 A watan Afrilun da ya gabata ne, kungiyar ta gudanar da bikin aurar da zawarawa 100 karo na farko a Masallacin Al-Mannar da ke Unguwar Rimi.