Bayan nan sai ku fara gabatar da wasanni masu motsa sha’awa, inda a nan ne wasu kan yi amfani da fina-finan batsa. Sai dai kafin lokacin akwai addu’ar da ake so ango ya gabatar.
Addu’ar da ango zai yi wa matarsa lokacin da ta shiga wajensa a daren angwanci:
Bayan ango ya dafa ko tava kan amarya, sai ya yi addu’ar kamar yadda shari’a ta tanadar: “Allahumma inna’as’aluka khairaha wa khairama jabaltha alaihi wa a’udhu bika min sharri ha wa sharri ma jabaltha alaihi.”
Fassara: “Ya Allah ina roqonKa alherinta da alherin da ka hallice ta a kansa, kuma ina neman tsari daga sharrinta da sharrin da Ka hallice ta a kansa. (Abu Dawud da Ibn Majah da Ibn Sinni suka rawaito).
To bayan nan sai ku fara gudanar da wasannin masu motsa sha’awa. Tun da Allah (SWA) Ya ce: “Idan mata da miji suka kalli juna cikin jin daxi da sha’awa, to Allah Zai kalle su cikin tausayi da kuma rahama.” Ana so ma’auratan su gudanar da wasannin na mintoci kafin su gabatar da jima’i, sai dai kafin saduwarsu akwai wasu addu’o’i da ake gabatarwa ko karantawa.
Ga addu’ar kamar haka: “Allahumma jannibnash shaixana wa jannibbish shaixana ma razaqtana.”
FASSARA: “Ya Allah Ka nesantar da ni daga shaixan kuma Ka nesantar da shaixan daga abin da Ka azurtamu da shi (Na ’ya’ya), (Bukhari da Muslim ne suka fitar da shi daga Abbas).
Idan Allah Ya qaddari samuwar xa a tsakani, to babu abin da zai cutar da shi. Hakazalika, bayan an kammala ibadar aure ma akwai addu’ar da ake gabatarwa. Ga addu’ar:
“Allahumma lataj’al shaixana fiyma razaqtani nasiban.”
FASSARA: “Ya Allah Kada Ka sanya shaixani ya zamo yana da rabo cikin abin da Ka azurtamu.(Bukhari da Muslim).
Rashin karanta waxannan addu’o’in kan sa a haifi yara marasa tarbiyya. Waxannan addu’o’i na kafin da bayan kammala jima’i, ba wai sai a daren angwanci za a yi kawai ba, har da sauran ranakun da ma’aurata suke saduwa.
A qarshe ina kira ga waxanda suke shirin yin aure da ma’aurata sabbi da tsoffi da su guje wa kallon tsiraicin junansu, bare na fina-finan batsa, duk da cewar kallon tsiraicin junan ma’aurata ba haramun ba ne, amma Annabi (SAW) bai tava kallon tsiraicin matansa ba, haka su ma ba su tava ganin nasa ba.
Baya ga haka Annabi (SAW) ya kwatanta nuna tsiraici ga ma’aurata, tamkar yadda jakai da karnuka suke yi ne a gaban jama’a, wanda kuma na san ba ma’auracin da ba zai ji kunyar saduwa a bainar jama’a ba.
Wasu malamai sun ce kallon tsiraicin junan ma’auarata na iya sanya a haifi makahon yaro ko yaro marar tarbiyya da kunya, kuma hakan zai iya rage qarfin idon ma’aurata. To in kuwa haka ne, ina ga masu kallon tsiraicin wasu, ballantana a sanya fina-finan batsa ana kallo ?
Wani abu na takaici kuma shi ne, a fina-finan batsar da ake sanyawar har da saduwa ta dubura, wanda hakan ke sanya ma’auratan saduwa ta dubura. To Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda ya sadu da matarsa ta dubura, a ranar sakamako Ubangiji (SWT) ba Zai kalle shi ba, kuma zai kasance cikin tsinuwar Ubangiji. Don haka nake kira don a ji a faxaka, don kauce wa faxawa ramin halaka. Ina kuma kira da a tashi tsaye don neman ilmin addini. Allah Ya ba mu ikon fin qarfin zuciyarmu, amin.
Daren farko ga ma’aurata (2)
Bayan nan sai ku fara gabatar da wasanni masu motsa sha’awa, inda a nan ne wasu kan yi amfani da fina-finan batsa. Sai dai kafin…