✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darasi ga Gwamnonin Arewa

Editan Aminiya ka ba ni dama, in yi tsokaci kan siyasar Najeriya. Jifar da aka yi wa su kwankwaso wajen ziyarar da suka kai wa…

Editan Aminiya ka ba ni dama, in yi tsokaci kan siyasar Najeriya. Jifar da aka yi wa su kwankwaso wajen ziyarar da suka kai wa Gwmanan Jihar Ribas, rotimi Amaechi, ta tabbata kasar nan ba a son zaman lafiya. Kuma wannan fada ne da al’ummar Arewa. Tunda Shugaba Jonathan ya dage kan lallai sai ya koma a shekara ta 2015, lallai al’ummar Arewa mu dauki mataki. Wajibi ne muhimmatu wajen neman zabin Allah. Domin wannan zabin da manyanmu suka yiwo mana babu mai jin dadinsa a Najeriya.
Tabbas gwamnonin Arewa sun ga babban darasi. Ina fatan sun san wanda ya sanya a jefi bakinsa. Da fatan kun koyi darasi. Talakawa kuma wajibi ne ku yi fafutika a ba ku abin da kuka zaba. Yau abin da ke faruwa a kasar Masar ya isheku darasi. Mu guji zalunci, kada mu goya wa azzalumai baya. Allah Zai yi mana agaji.
Daga Sharhabilu dan Mai littafi, Kiri kasamma.

Sakonnin waya

A kyale Al-Makura ya yi aiklinsa
Assalamu alaikum. Ina kira ga ’yan majalisar Jihar Nasarawa da su bar gwamna ya yi aikinsu, su kawar da bambancin siyasa, domin ci gaban Jihar Nasarawa. Daga Alaramma Uban dalibai. Ma’assalam 08052659678.

Aminiya kina wayar da kai
Salam. A gaskiya Aminiya kuna wayar mana da kai a kan dimokuradiyya. Allah Ya kara daukaka ku, ku ci gab da wayar mana da kai. Daga Abdullahi Mai kifi Zaria Road. 08058413421.

Mata ku ji tsoron Allah
Sallam. Don Allah ina rokon Editan Aminiya ka bani fili in mika sako nag a mata. Mata kun zama kaji domin watsi ke yi muku, mu maza mun sani. Idan ba mu tanadi tsabar watsa wa kaji ba, don Allah mu je mu samu tsabar. Don wannan zamani kaji amsu tsaba suke biya. Mata ku ji tsoron Allah. Daga Chuwa-Chuwa Sufa Sita. 07086259799.

Samari ku ji tsoron Allah
Aminiya ina fatan za ki buga sakona. Don Allah samari a daina yaudarar ’yan mata. Ku ji tsoron Allah. Duk wanda ya zalunci wani, sai Allah Ya yi masa sakaya. Kada ku ga Allah bai saka mana anan ba, ku dauka kun ci riba. Wallahi babu riba a ciki. Daga Aminah Abubakar Teke 08172601395.

Addu’ar neman zabi ce mafita
Duk mi son ta gane mayaudari a cikin samari, to ta koma ga Allah. A rika yin addu;ar neman zabin abin da ya fi dacewa a cikin rayuwa da addini. Allah Ya yi mana zabi mafi alkhairi. Daga Bello  Ruma 08076922842.

’Yan mata a kiyayi Allah
Edita ka ba ni gurbi in yi kira   ga ’yan matan wanan zamani, musamman ’yan uwana Musulmi su daina shiga da kwalliyar masu badala mawakan Amurka. Wannan kwalliya ta samu karbuwa a kasar Musulmi, kauyuka da birane, musamman a kasata Najeriya. Daga Maryam Aliyu Garko, Kano 08156589750..

Mata a rage buri
Salam Aminiya ina kira ga mata da su rage buri wajen yin aure, su sani arziki na Allah ne, kuma su san yawancion wadanda suke ganin mazajensu da kudi sun samu kudin ne bayan sun yi aure. A yau idfan aka ce mace ta yi sa’ar miji kana dubawa sai ka ga mai kudi ake hange ba a maganar mutunci. Shi yasa ake samun matsaloli yandu cikin zamantakewar aure. Daga Ahmad Rufa’I Kano 08166667703.

Ga samari da ’yan mata
Assalamu alaikum. Zuwa ga Aminiya, ba ku taba buga sakona ba. Don Allah ian so ku ba no dama in ja hankalin ’yan amtan wannan zamani. Wallahi mu ji tsoron Allah, ‘Yan uwana mata da samari; mu farka daga barci, rayuwarmu akwai matsala. Mu tanadi dadadan maganganun da za mu fuskanci Ubangijinmu da su. Da fatan Allah (SWT) ya ba mu ikon kiyayewa. Daga Nuruddeen Isma’il Gusau, Jihar Zamfara 08105096009.

Ga Katsinawa
Hukumar kididdiga ta kasa kin ja mana fitina a Katsina, tun ranar da aka ce Katsina ce ta biyu wurin talauci, masu kananan sana’o’i muke cikin ukuba. Daga Kado Abba Mobil KT. 08059128416.

A kwashe sharer Suleja
Akwai bukatar karamar hukumar Suleja ta kara kokari wajen ceto garin Suleja daga annobar shara da ta yi wa garin katutu a kowane lungu da sako. Daga dahiru Dauda (KGY) Bindawa 08055552897.
Ga amgoya bayan APC
Salam Magoya bayan APC da shugabanni a daure a hada kai, domin ci gaban jam’iyya. Daga Sulaiman SBK Kano 07038999155.

Najeriya ba tsaro
Tura sojoji kasar Mali abin kunya ne ga Najeriya. Ba tsaro a gida kuna tura soja Mali. Daga Auwalu Musa Ibrahim Warure Kankwana. 08097511478.

Jinjina ga bision FM
Ina jinjina wa Gidan Rediyon bision FM da kwararrun ma’aikatansu. A gaskiya shirye-shiryenku na burgeni. Ga fede gaskiya komin dacinta. Da fatan Allah Ya daukaka mu baki daya. Daga AA Sarki Kakumi, Apo Garki, Abuja 08078325069

Ga Jirgin talakawan Funtuwa
Assalam. Aminiya ina so Edita ka ba ni dma in mika gaisuwata ga jirgin talakawan Funtuwa, Muntari dan Dutse, tare da mika gaisuwata ga iyalan Garba na Funtuwa rashin matarshi da ya yi da fatan Allah Ya jikanta. Amin. 07064979105.
.
Ga ‘yan NEPA
Salam Aminiya na dade ina neman hanyar jan hankalin ’yan NEPA, musamman ’yan NEPAN GML. Ina mamakin yadda suke kokarin mayar da FML wajen wasa buyan yara saboda tsabar duhu. Kuma sai wata ya yi, sai ku kawo tayi sa’o’i biyu, shi ma don ku karbi kudin wuta ne. Ku ji tsoron Allah. Daga Maharazu GML, Abuja ktrs. 08153285492
.
Bauchi Allah Ya yaye
Assalamu alaikum. Mu kan mun shiga uku a Bauchi, ba wuta, ba ruwa ga talauci. Allah Ya yaye mana wannan musifa, amin. Daga Naziru Nanaye,Jahun Bauchi na Hauwa. 08071876788.
Mu guji fushin Allah
’Yan uwa Musulmi. Mu guji aikata manyan zunubai masu wanzar da fushin Allah. Ba mutuwa ba ce abin tsoro, mutuwa babu imani. Mu rika tuna mutuwa a kodayaushe. Daga Maman AbdulBasit, Gombe 08125518587.

Addu’ar cin jarabawa
Don Allah Editan Aminiya ka mikwa min sakiona zuwa ga masoyan Aminiya su taya ni da addu’ar samun cin jarabawar kualifying. Daga kanwar Mai Kawo Kano 08057947801

A kara shafin sakonni
Editan Aminiya sai ka kara yawan shafin sakonnin waya, tund amarubuta sun karu. Daga Ibrahim AB Balarabe Birnin Zariya. 08023442901.

Gwamna Lamido ya yi gyara
Aminiya ku ba ni dama in gaida gwamnan gwamnoni, babban siyasa, kan yadda ya gyara Jigawa. Sai ya yi shugaban kasa in sha Allah. Daga Khalid Garkuwa B/Kudu, Jihar Jigawa. 08068992841.