✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Darajar kudin Rasha na Ruble ta karu

Ruble ta yi darajar da ba ta taba kai wa ba a cikin shekaru bakwai a kan kudin Yuro.

Darajar takardar kudin Ruble na kasar Rasha ta kai matsayi mafi girma da ba ta taba kai wa ba a cikin shekaru bakwai a kan kudin Yuro.

Kudin na Ruble wanda tsadar man fetur da iskar gas ta sa ya yi tashin goron zabi a kasuwannin hada-hada na kudi, ya haura da sama da kishi 20 cikin dari a gaban kudin Yuro fiye da lokacin da aka soma yin yakin.

A halin da ake ciki kamfanoni da yawa na Turan ya zame musu dole kanwar naki, wajen bin umarnin Putin na yin cinikayyar a Rashar da kudin Rubel.

Kudin Rashan shi ne kudin duniya wanda ya fi samun ci gaba fiye da kowanne tun farkon shekara.