✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dani Albes ya fara shirin barin kulob din FC Barcelona

Dan kwallon baya a kulob din FC Barcelona na Sifen kuma haifaffen Brazil mai suna Dani Albes ya fara shirin barin kulob din bayan kwantaraginsa&nbsp…

Dan kwallon baya a kulob din FC Barcelona na Sifen kuma haifaffen Brazil mai suna Dani Albes ya fara shirin barin kulob din bayan kwantaraginsa&nbsp ya kare a kakar wasa ta bana.
Kwantaragin dan kwallon za ta kare ne a watan Yuni mai zuwa kuma kawo yanzu kulob din bai yi wani yunkiri don kara masa wa’adi ba.
Tuni ajent din dan kwallon mai suna Dinorah Santana ya ce akwai yiwuwar dan kwallon ya tarkata komatsansa ya bar kulob din a kakar wasa ta bana ganin kawo yanzu kulob din bai tuntubi dan kwallon don ya sabunta kwantaraginsa ba.
Dani Albes dai ya shafe kimanin shekara bakwai yana yin kwallo a FC Barcelona tun bayan ya canza sheka daga kulob din Sebilla da ke Sifen.
Idan za a tuna Hukumar kwallon kafa ta Sifen ta kakaba wa Barcelona takunkumin saye ko sayar da ’yan kwallo na tsawon shekara guda bayan an samu kulob din da yin magudi a wajen cinikin matasan ’yan kwallo a shekarun baya al’amarin da ya sa Daraktan kulob din Andoni Zubizerrata ya yi murabus a watan Disamban bara.&nbsp Daga bisani tsohon kyaftin din kulob din Carlos Puyol shi ma ya yi murabus don goya wa Daraktan baya.