✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangote zai tallafawa mata dubu 106 da sama da Naira biliyan 1

Gidauniyar Dangote, mai suna Aliko Dangote Foundation, ta shirya tallafawa Mata kimanin dubu 106 da kudade sama da Naira biliyan 1.1 a jihohi hudu na…

Gidauniyar Dangote, mai suna Aliko Dangote Foundation, ta shirya tallafawa Mata kimanin dubu 106 da kudade sama da Naira biliyan 1.1 a jihohi hudu na Arewacin kasar nan.

A yunkurinta na tallafawa Mata, gidauniyar ta fara tantance wadanda zasu amfana da shirin domin ganin an bunkasa rayuwar mata a jihohin.

Wadanda zasu amfana sun hada da Mata dubu 23 a jhar Sakkwato, sai Mata dubu 34 a jihar Katsina, da Mata dubu 21 a Kebbi, da kuma Mata 28 a jihar Zamfara.

Shirin dai ya kuduri aniyar bada tallafin kudi Naira Biliyan dubu 10 ga Mata kimanin Miliyan 1 a fadin kasarnan, inda aka fara gunar dashi a garin Kano a shekarar 2011. Kuma ana saran shirin zai ci gaba da gudana har zuwa kowanne sashe na Kananan Hukumomi 774 da ke kasar nan.