Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko dangote Ya samu karin Dala biliyan tara da miliyan dari biyu a shekarar 2013 wanda ya sanya ya zama na 30 a jerin masu kudin duniya.
Mujallar Bloomberg wacce ke bibiyar hada-hadar kudi da kasuwanci a duniya ita ta bayyana haka, inda ta bi sahun mujallar Forbes wacce ta ba da rahoton cewa dangote ya sami riba mafi yawa wanda hakan ya sa ya zama attajirin daukacin nahiyar Afirka kuma na 42 a jerin attajiran duniya a shekarar 2013.
Mujallar ta bayyana cewa hamshakin dan kasuwan nan mai kamafanin Microsoft Corps, Bill Gate shi ne ya fi kowa samun riba a shekarar 2013 a duniya baki daya, inda ya samu fiye da Dala biliyan 78 kari.
Mujallar ta ruwaito cewa, masu kudin sun kara samun kudi, inda suka samu jumillar Dala biliyan 524 a shekarar 2013.
Ta kara da cewa, a cikin attajirai 300 da sunayensu ya samu shiga cikin jerin sunayen attajiran duniya, mutum 70 ne kawai a cikin su suka samu asara a cikin watanni 12 da suka gabata.
Mujallar ta bayyana cewa, dangote ya samu riba mai yawa a siminti wanda shi ne kamfani mafi karbuwa a kasuwar hannayen jari ta Najeriya da kashi 74 cikin dari na daukacin hannayen jarin da aka saya.
Ta ci gaba da cewa, kididdiga ta nuna cewa dangote ya mallaki dala biliyan 22 da dubu dari tara a kan Dala biliyan 12 da dubu dari takwas da ya mallaka a karshen watan Disamban shekarar 2012.
A yayin da yake kara fadada harkar simintinsa a nahiyar Afirka, dangote ya fada harkokin tace albarkatun danyen man fetir inda ya shiga yarjejeniya da wadansu kamfanonin ciki da wajen Najeriya, inda zai gina wata katafariyar matatar mai da masana’antar takin zamani mafi girma a Najeriya a kan Dala biliyan uku da talatin.
Matartar man za ta lashe Dala biliyan tara kuma za ta samar da guraben ayyukan yi kimanin dubu 25 tare da tace gangar danyen mai dubu 400 a kullum.
dangote ya bayyana cewa kamfanin takin zamanin zai rika samar da tan miliyan biyu da dubu 800 na taki wanda hakan zai taimaka wajen bunkasar noma a Najeriya da nahiyar Afirka baki daya.
Dangote ya rike kambunsa na attajirin Afirka
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko dangote Ya samu karin Dala biliyan tara da miliyan dari biyu a shekarar 2013 wanda ya sanya ya zama…