✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangote ya haskaka a Kasuwar Baje-koli ta Legas …Abokan ciniki da dillalai da ’yan makaranta sun yi tsinke wa rumfunan kamfanoninsa

A yini na uku na fara cin kasuwar baje-koli ta duniya da ake gudanarwa a Legas, rukunin kamfanin Dangote ya mamaye kasuwar da nuna irin…

A yini na uku na fara cin kasuwar baje-koli ta duniya da ake gudanarwa a Legas, rukunin kamfanin Dangote ya mamaye kasuwar da nuna irin kayayyakin da yake sana’antawa.

Kuma sakamakon sanarwar da ya rika bayarwa kafin fara cin kasuwar ta shekara-shekara, abokan ciniki da masu ziyara sun rika tururuwa zuwa rumfunan kamfanonin Dangote da aka baje irin kayayyakinsa inda masu saye suka kwasar garabasa a daidai lokacin da kuma ake ba jama’a kyautar wasu nau’o’in kayan a matsayin dandano don jawo hankalin abokan ciniki.
Rumfar kamfanonin da ke kusa da babbar kofar shiga cikin Dandalin Tafawa balewa da kasuwar ke ciki ta ba maziyarta damar fara ido hudu da kayayyakin kamfani yayin shiga kasuwar yayin da masu rawa ke burge ’yan kallo.
Yara ’yan makaranta da malamansu daga makarantu daban-daban na jihar sun halarci rumfar domin ganin irin kayayyakin da yake yi inda aka rika ba su kyaututtuka daga kamfanin.
Kamfanonin da suka baje kayayyakinsu daga rukunin kamfanonin Dangote sun hada da kamfanin siminiti na Dangote da kamfanin sukari na Dangote da na yin fatun buhu da na gishiri (NASCON) da kuma na yin kayan marmari na Dansa Foods Limited, daya daga cikin kamfanonin da ke sahun gaba wajen yin abincin gwangwani da nau’o’in lemon kwalba.
Wurin da ya fi jan hankalin jama’a shi ne dakin abinci na Dangote, wanda ya rika ba da kyautar nau’o’in dafaffun abinci da kamfanin yake dafawa ga abokan ciniki.
Maziyarta rumfar sun kuma rika samun kyautar ababen sha na Dansa, lamarin da ya jawo kwararar masu son sayen kayayyakin kamfanin, yayin da wadanda ke son zama dillalai suka rika yin rajista a rumfar.
Shugaban sashin hulda da jama’a na kamfanin Anthony Chiejina, ya ce shigar rukunin kamfanonin a dama da shi a kasuwar wata dabara ce ta dada kusato kamfanin ga dillalai da abokan cinikinsa.
Ya shaida wa manema labarai a harabar kasuwar cewa kamfanin shi ne bangarorin kamfani da shi ne mafi girma a Nahiyar Afirka sun halarci kasuwar ce da zimmar kara rike kambinsu na jagora a fannoni daban-daban tare da kara wa abokan cinikinsu kwarin gwiwa kan irin kayayyakin da suke yi.
“Mazu ziyartar rumfunan rukunin kamfanin a kasuwar za su samu damar sayen kayayyakin kamfanonin a farashi mai rahusa. Kuma akwai samfurin kayayyakin da za a ba su. Wasu daga cikin bangarorin kamfanin sun bullo da shirye-shiryen karbar dalibai a wasu ranaku. dalibai masu ziyara ga rumfunan za a ba su kyaututtuka na musamman kamar biro da fensuri da littattafan rubutu da sauransu,” inji shi.