Wata takaddama ta kunno kai tsakanin Gwamnati da kuma Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), kan binciken da hukumar ke yi kan wasu kwangiloli da aka bai wa wasu iyalan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Bayanai sun ce hukuncin da shugaban PCACC, Muhuyi Magaji Rimin-Gado ya yanke na binciken kwagiloli ciki har da na wata Cibiyar Yaki da Cutar Daji da aka bai wa ’yan uwan gwamnan ce ta janyo takaddamar.
Muhuyi wanda ya tabbatar da binciken da hukumar da yake jagoranta take gudanarwa, ya ce babu wata manufa da suke da ita a kan iyalan Gwamnan, kuma babu wanda za su raga wa muddin aiki ya biyo ta kansa.
A makon da muke ciki ne wasu rahotanni suka bayyana cewa Gwamna Ganduje na shirin sauke Rimin-Gado daga mukaminsa, har ya fara yi wa Majalisar Dokokin Jihar matsin lamba a kan bukatar hakan.
Aminiya ta ruwaito cewa, a yayin da Majalisar ke shirin fara gudanar da bincike a kan Rimin-Gado, tuni Gwamnatin Jihar ta tura wani jami’i daga Ofishin Akanta-Janar na Jihar ya maye gurbin Akantan Ofishin na PCACC.
A yayin da wakilinmu ya tuntube shi, Rimin-Gado ya ce yana maraba da binciken da za a gudanar a kansa, sai dai kuma ba zai lamunci a maye gurbin jami’in hukumar da wanda Gwamnatin Jihar ta turo ba saboda yin haka huruminta ne ba na gwamnati ba.
Sai dai hakar Aminiya ba ta cimma ruwa ba wajen neman jin ta bakin Sakataren Yada Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Abba Anwar, domin ji daga bangarensa.