Taya al’ummar musulmai murnar bikin Babbar sallah da wasu mabiya addinin kirista suka yi, abin ayaba ne. Hakan na nuna akwai kyakkyawar alaka da fahimtar juna tsakanin mabiya addinin islama dana kirista a kasar Najeriya. Matsalar kawai yan’siyasa na amfani da bambacin addinan wajen rabo kawunan mu, domin su cimma buri kansu na siyasa. Daga Mansoor Said PRP Kano. 07039215954 .
Ga Masarautun Kebbi
Edita ina kira ga yan siyasar Jihar Kebbi da su yi juna masalaha, su kumakyale masarautar Gwandu ta ci gaba da mulkin Jihar Kebbi, domin ita ke da tarin ’yan siyasa da ’yan boko, ga kuma kwararrun malamman addini, wadanda idan aka yi la’akari da wannan babu wata masaruta da ta kai Gwandu, inda take da kananan Hukumomi 10 a cikin 21 da ke fadin jihar Kebbi. Shi yasa nike kira ga sauran masarautun Yauri, da Zuru, Argungu da mu hada kai mu ci gaba da zaman tare da muka gada daga mujaddadi Abdullahi Gwandu. Da fatan Allah ya kara hada kanmu baki daya. Daga Usman Adamu Aliero, Jihar Kebbi. [email protected] 07061594299.
Godiya ga Kabiru Gaya
Ina jinjina wa sanatan kano ta kudu Alhaji Kabiru Ibrahim Gaya bisa kokarin da yake yi na gudanar da ayyukan alheri ga al’umar Jihar Kano baki daya. Gaskiya muna matukar jin dadin yadda kake aikace-aikace a fadin Jihar kano ba wai sai a Kano ta Kudu kadai ba, har ma da sauran mazabun Kano ta tsakiya da kano ta Arewa. Muna fata Allah ya kara masa daukaka zuwa matsayin gwamnan.
Jamilu Abdullahi Bichi, Jihar Kano: 08039434980 [email protected]
Lukman alheri ne a Kaduna
Edita ka ba ni dama in nuna wa al’ummar Jihar Kaduna fa’idar da ke tattare da zaben Salihu Lukman a matsayin Gwmnan Jihar Kaduna, musamman a daidai lokacin da zaben 2015 ke karatowa. Salihu Lukman ya yi gwagwarmayar kwatar ’yancin talakawar kasar nan, musamman a kungiyar daliban Najeriya ta NANS, cikin shekarun 1980, inda aka taba daure shi saboda hakkin al’umma. Irin wannan gwarzo idan ya kama ragamar mulki, sai talakawa ya sa ransa a inuwa. Sai mu yi tunani. Allah Ya yi mna zabi nagari. Daga Rabi’u Yusif Dodo 08053534000.
Ga Talakawan Kaduna
Assalamu alaikum. Ina kira ga talakawan Jihar Kaduna, ku zo mu hada kai mu zabi Mukhtar Ramalan Yaro, a matsayin Gwamnan Kaduna. Daga Director 07054702411.
Godiya ga Gwamna Shettima
Godiya ta musamman ga Gwamnan Barno, Kashim Shettima. Ina mika wannan godiya ne a matsayina na dan karamar Hukumar Biu da ke Jihar Barno, bisa sayen motocin tsaro 40 da ka bai wa ‘’yan sanda,kuma sufeto Janar (IGP) ya ce kai ne na farko da ya yi wannan gagarumin aiki. Allah Ya baka damr ci gaba dadawadannan ayyuka nagari. Daga 08030818197.
Sojojin Turawa a Afirka?
Al’ummar Afrika mu yi kaffa-kaffa wajen amincewa da girke Sojojin kasashen Turawan Yamma a cikin kasashenmu, wai da sunan samar da tsaro ko yakar ‘yan ta’adda. Musamman kasashen Amurka da Faransa da kuma Ingila. Su kansu Turawan na fama da matsalolin a yankunansu. Mu nemi hanyar tattaunawar masalaha wajen warware matsalolinmu. Allah Ya shige mana gaba. Amin. Daga AbdulMalik Sa’idu Mai Biredi, Tashar Bagu, Gusau 08069807496.
Addu’a Ga kasarmu
Allah ya kawo mana karshen tashinar da ya addabi Jihar Borno, dama sauran sassan kasar mu Najeriya Baki daya amin. Daga Adamu Aliyu Ngulde 08032135939.
A ceto ’yan matan Chibok
Tabbas ya cancanta ‘yan majalisar tarayya su matsa wa Gwamnatin Najeriya lamba, domin ta dauki matakin ceto ‘yan matan Chibok daga hannun ‘yan boko haram. Ga shi har sun yi wata shida babu abin da aka yi a kan matsalar.
Daga Ababakar Lawal Gidan Danmaye a Jargaba +2348097627776.
Ga mahukuntan Najeriya
Gaskiya farmakin da Sojojin Najeriya sunka kai a Unguwar Durumi, ta marasa galihu a Abuja abin ya saba wa mizanin hankali, don gaskiya bai kamata a ce sojojin Najeriya suna maida rayuwar al’umma tamkar rayuwar naman daji ba. Kwanakin baya kowa ya ga yadda sojoji suka yi wa wadanda ba su ji, ba ba su gani ba kisan gilla a Unguwar Apo da ke Abuja. Don haka nuna kira ga mahukuntan Najeriya da cewa, ya kamata su gaggauta yin bincike da kuma hukuntan wadannan Sojoji. Don bai kamata a ce sojojin Najeriya suna yi wa al’umma kisan gilla ba.
Daga Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi, jihar Kebbin Najeriya. GSM 07037697009.
Zaluncin ’yan taskforce a Abuja
Editan wannan jarida, ka isar da kukanmu ga mahukunta kan yadda ‘’yan taskforce ke nuna bambanci wajen kama masu tallace-tallace a Abuja. Kuma suna yi wa mutane kwace da zalunci,don kafin a a kai mutum ofis, sai kawai su lalube masa wayar hannu da kudi. Edita muna rokonka da sauran kafafen yada labarai da a gudanar da bincike kan wadannan ma’aikata. Idan kuma hukuma ce ta umarce su ko taba su damar zalunci, to sai mu ci gaba da neman taimakon Allah a kansu. Domin zaluncin ya isa haka nan. Kuma wannan wacce irin wauta ce, sai daidai lokacin zabe gwamnati za ta sa a rika musguna wa talaka. Ko dai abin za a ci gaba da yi ke nan; ko wannan ce dimokuradiyyar taku? Daga Murtala Ushar Kabo, Kano, mazaunin Abuja. 08137996396.
Ga Gwamnatin Yobe
Don Allah Aminiya ku share min hawayena, wajen Isar min da kirana zuwa ga Gwamnatinmu Ta Jihar Yobe da ta yi wa Allah ta soke matsayin da ta dauka na korar kananan ‘yan kasuwa a manyan hanyoyi hudu da ke Birnin Damaturu, domin matakin zai raba jama’a da dama da sana’o’insu. Daga Usman bin Affan ibn Adam Damaturu.
Addu’a ga Najeriya
Edita ka b ani dama in mika addu’a ta ga Najeriya, ganin muna tunkarar zaben 2015. Allah Ka zabar mana shugabannin kirki, masu tausayi, masu son kasar nan. Allah ka hada kan kasar nan. Kada ka ba mu wawayen shugabanni. Amin. Daga 08075959086.