✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dandalin fim: Abin alherin da ya zo da matsala -Kasagi-Na-Halima

Umaru danjuma Katsina wanda aka fi sani da Kasagi Na-Halima ba boyayyen suna ba ne a masana’antar fim din Hausa kasanacewar ya shafe tsawon shekara…

Umaru danjuma Katsina wanda aka fi sani da Kasagi Na-Halima ba boyayyen suna ba ne a masana’antar fim din Hausa kasanacewar ya shafe tsawon shekara 40, a harkar wasan kwaikwayo da fina-finai, a tattauanawarsa da Aminiya ya yi bayani kan hanyar da ya kamata a bi domin ganin an tabbbatar da Alkaryar Fina-Finai kamar yadda gwamnati ta kuduri yi:

 

A kwanakin baya Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar janye gina Alkaryar Fina-Finai da ta kuduri ginawa a Jihar Kano sakamakon sukar da ya fuskanta daga jama’a mene ne ra’ayinka a kan wannan batu?
Abin da ya jawo faruwar hakan shi ne irin tofin Allah tsine da malaman Jihar Knao suka yi wa lamarin, babu shakka malamai suna da hujjar da za su yi hakan. A farkon lamarin da aka fara fina-finan Hausa, yanyin yadda ake gudanar da fina-finan ya saba da al’adun Hausawa. Masu yin fina-finan ba su kula da al’adu da shi kansa harshen Hausa. Wannan shi ne ya sa malaman suka tayar da waccan magana. Kodayake a wani bangaren samun masana’antar fina-finan Hausa alheri ne ga kowa.
Ta wacce hanya ya zama alheri ga kowa?
Wannan aiki dai sabo ne da zai lashe biliyoyin Naira wanda za a gina shi a Arewa, ba don ya zo da tangarda ba, la’akari irin kudin da za a kashe a wannan aiki an san abu ne  da zai bunkasa garin da za a gina dandalin da kuma tattalin arzikin yankin gaba daya. Abu na biyu kuma shi ne idan har ba a gina danadalin ana Arewa ba, to ’yan Kudu sun samu garabasa. Don haka yin abin a Arewa, musamann Kano na tabbata zai kara bunkasa arzikin wannan bangare. Abin da ya kamata a yi shi ne a nuna wa jaruman yadda ya kamata su gudanar da abubuwansu da abin da ya kamata su nuna a fina-finansu da kuma wanda bai kamata ba. Duk wanda ya ji yawan kudin da za a kashe a wannan aiki zai ji tsoro ganin irin abubuwan da masu fina-finan nan suka yi a baya. Idan ka duba fina-finansu ka san cewa fina-finan Indiya suke kwafa, wadanda kuma sun saba wa addini da al’adunmu na Hausawa. Indiyawa suna ciyar da al’adunsu gaba ta hanyar fina-finansu haka Turawa. Suna fadin cewa mu Hausawa ba mu da al’adu da dabi’un da za mu nuna a fina-finanmu? A da mun yi wasanni irin su Ruwan Bagaja da Kulba na barna da Babban Larai da Magana Jari. Idan ka duba, wadannan wasanni za ka ga yadda suke nuna kyawawan al’adun Bahaushe.
Idan muka yi la’akari da yadda rayuwa take canzawa, ba ka ganin ya kamata a samu irin wannan canjin a harkar fina-finan Hausa?
Wane zamananci kuma? Ai ko Indiyawan da muke kwaikwayo sun dade suna kokarin ciyar da al’adunsu gaba, kafin daga bisani su dan kauce hanya kadan, domin a da ba za ka taba ganin tsiraicin Indiyawa mata ba. To mu ba mu yi haka ba, sai ga shi cikin lokaci kadan muna kokarin kauce wa al’adunmu tare da kwafo na wasu.
A tunnanika wane irin alfanu wannnn aiki na dandalin fim zai haifar idan da za a aiwatar da shi?
Daga yadda na samu labari abin zai zama wata hanya ta samun kudin shiga ga gwamnati, abin da kasar nan take matukar bukata. Abu na biyu za a samu aikin yi. Da a ce matasan da ke shirya fina-finan nan za su dawo hanya bisa kula da al’adun Hausawa to na tabbata hakan zai yi amfani matuka. Idan har gwamnati ta shigo ciki ta aiwatar da wannan shiri na dandalin fim, hakan zai taimaka wa tattalin arzikin Kano da kuma samar da ayyukan yi.
Me kake tsammani daga Shugaban kasa tunda an janye wannan shiri a Kano?
Shawatara ita ce kada Shugaban kasa ya soke shirin gaba daya, dubi da matukar amfanin da yake da shi kamar yadda na yi bayani a baya. Wadansu mutane na tunanin da gwamnati ta sanya kudin cikin wata harkar ta daban, duk da cewa suna da dalilansu. To amma wadannan abubuwa ne daban-daban masu zaman kansu.
Sai dai malamai duk sun yi tofin Allah tsine ga lamarin?
Akwai malaman da suke da fahimtar lamarin. Akwai wani malami a nan Katsina wanda koyaushe idan muka hadu yakan ce “Alhaji Umar Kasagi ina irin naku wa’azin. Kun bari an fi tsoron irin naku, mu yanzu ba a sauraronmu.” Idan ya fadi hakan mukan yi dariya. Abin da ya tsorata malaman nan har suka dauki wancan mataki shi ne idan har aka ba masu fim irin wannan dama to fa za su ci gaba da cin karensu ba babbaka. Sai dai akwai hanyar dakile faruwar hakan ta hanyar nuna wa masu fim din nan yadda za su rika yin fina-finansu ta yadda za a wayar musu da kai tare da dora su kan abin da ya dace. Lokacin da muke a Cibiyar Al’adu ta kasa mun yi diploma inda hakan ya taimaka mana wajen gudanar da ayyukanmu. Ina kira ga gwamnati ta kara bayar da damar samun horo kan fim a jami’a da Kwalejin Talabijin da ke Jos.
Tunda mutanen Kano sun yi tir da al’amarin kana ganin ko a mayar da shi Katsina ko wasu wuraren na Arewa?
Babu hanyar da mutanen Kano ba za su so wannan lamari ba ganin yadda gwamnati ta shiga cikin lamarin. Kuma babu yadda za a yi ka gaya min cewa na rufe wani ofis nawa, wanda kuma na yi rajistarsa ina harkokin kasuwancina. Mafita ita ce kawai a ilimintar da ’yan fim din a kan abin da ya kamata su yi da kuma abin da ya kamata su gujewa. Mun sani cewa fim shi ne nuna yadda rayuwar al’umma take. Sai dai masu fim din sun dan kauce, don haka akwai bukatar a gyara musu. Yawancinsu ba su da horo game da harkar fim, sai dai kawai a wayigari ka ga mutum ya zama ba tare da sanin abin da ya kamata darakta ya zama ba. Na samu horo a kan harkar fim a Birtaniya, kafin ka zama darakta sai ka zama ka san duk wani abu da ya shafi harkar fim da abin da ya shafi daukar hoto da rubuta labarin fim da tacewa da sauransu.
Ko wadannan su ne dalilin da suka sa ba ka fitowa a fina-finan Hausa?
Ba haka ba ne, ba su taba zuwa wurina da zimmar gayyata ta in yi musu wasa ba. Ina ganin Ishak Sidi Ishak ne kawai ya taba sanya ni a fim dinsa. Gaskiya ba haka ba ne, shekarata 40 ina wasan kwaikwayo. Mu ne mutane na farko da muka je Ingila muka samu horo a kan harkar fim. Bayan na dawo ne na rubuta littafin Kulba na barna wanda ya samu karbuwa a duniya, inda ya ci kyauta a Italiya da Faransa da Burkina Faso. Ba kushe musu nake yi ba, ina dai kawo hanyoyin da ya kanmata su bi wajen samun mafita ne.