✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Danboko

Wani matashi ne dan karya kuma danboko, ya kammala karatunsa amma ba aiki; ya yi ta kokarin neman aiki bai samu ba. Wata rana wani…

Wani matashi ne dan karya kuma danboko, ya kammala karatunsa amma ba aiki; ya yi ta kokarin neman aiki bai samu ba. Wata rana wani manajan kamfani ya ce ya je ya yi masa intabiyu, domin daukarsa aiki. Da ya je, ga abin da ya wakana tsakaninsu:
Manaja: Mene ne sunanka?
danboko: KF.
Manaja: Mene ne KF?
danboko: Kabir Faruk.
Manaja: Wane gari kake?
danboko: KF.
Manaja: Mene ne KF?
danboko: Kwanar Farakwai.
Manaja: Wace unguwa kake?
danboko: Ni fa komai KF ne.
Manaja: Mene ne KF?
danboko: kofar Fada.
Manaja: Wace makaranta ka yi?
danboko: KF.
Manaja: Me ke nan?
danboko: Kwalejin Fasaha.
Manaja: menene sana’arka?
danboko: KF.
Manaja: Mene ne KF?
danboko: Kota da Fartanya.
danboko: To ya labarin KF?
Manaja: Mene ne KF?
danboko Labarin kokarina Fa?
Manaja: To kai ma KF.
danboko: Ah! Manaja, mene ne kuma KF?
Manaja: Ka Fadi.
Daga Buhari Liman