✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan tsohon Shugaban Najeriya Abacha ya rasu

Abdullahi Sani Abacha ya rasu yana tsakar barci.

Daya daga cikin ’ya’yan tsohon Shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Sani Abacha ya rasu.

Abdullahi Sani Abacha ya rasu ne lokacin da yake barci a daren ranar Asabar, kamar yadda ’yar uwarsa, Gumsu Sani Abacha ta wallafa a shafinta na Twitter.

Gumsu wadda mai daki ce ga Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, ta wallafa cewa “Inna lilLahi wa inNa ilaiHi raji’un.

“Na yi rashin kanina wanda ya rasu yana tsakar barci.

“Allah Ya yafe masa kurakuransa Ya sa Aljannah ce makomarsa.”

Ta kara da cewa, za a yi jana’izarsa a Babban Masallacin Abuja sannan za a binne shi a makabartar Gudu da ke babban birnin na Tarayya.

Rahotanni sun ce Abdullahi Abacha wanda shi ne na biyun karshe cikin ’ya’yan marigayi Janar Abacha, ya mutu ne yana da shekara 36 a duniya.

Marigayin ya rasu ne a gidansu da ke Abuja babban birnin Najeriya.