✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘dan tawayen da ya kashe Sardauna ba dan Abakwa ba ne’

Marigayi Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogwu shi ne ya jagoranci juyin mulkin soja na farko a kasar nan, wanda ya yi sanadiyar mutuwar manyan ’yan siyasa…

Marigayi Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogwu shi ne ya jagoranci juyin mulkin soja na farko a kasar nan, wanda ya yi sanadiyar mutuwar manyan ’yan siyasa da sojoji kamar Alhaji Abubakar Tafawa balewa da Sardauna Ahmadu Bello da Birgediya Maimalari da Ademulegun da sauransu. Aminiya ta zakulo wani dattijo da ya san kuruciyar Manjo Chukwuma a garin Abakwa da ke Kaduna mai suna Abubakar Musa Abubakar, wanda ya yi mata karin bayani kansa:
 
Tun yaushe ka san Manjo Chukwuma Nzeogwu?
 Bayan da aka taso mu daga tashar jirgin Abakwa kusa da Kwalejin Gwamnati ta Kaduna, sai muka dawo inda Abakwa take a yanzu, inda kanen mahaifin Chukwuma da ake kira Anthony yake da gida kusa da makarantar firamare ta Abakwa. An fi sanin gidan da sunan Gidan Anthony, wanda shi ne shugaban ’yan kabilar Ibo a yankin.
 Shi kuma Chukwuma yana zuwa hutun makaranta wurin baffansa daga cikin garin Kaduna. Yana kuma binsa zuwa farautar tsuntsaye a dajin da ke gefen Abakwa wanda a yanzu aka gina makarantar horar da kananan hafsoshin soja (NDA). Saboda baffansa mafarauci ne yana da bindigar farauta kuma yana darajta kowa a yankin, shi ma ana daraj ta shi. Daga baya ne Chukwuma ya shiga makarantar kuratan sojoji da ke Zariya, inda lokacin da ake shirin bayar da mulki aka kai sun ingila don zama hafsoshi. Saboda a lokacin babu mutane da yawa kamar yanzu kuma ana darajta kowa ba kamar yadda abubuwa suka tabarbare ba a yanzu. Shi Chukwuma matashi ne shiru-shiru. Zuwan da Sarauniyar Ingila ta yi a 1956 a lokacin ana shirye-shiryen mika mulki, ya sa a kai yi ta daukar jama’a aikin gwamnati wanda ya kai ga fara yin zaben ’yan majalisa na farko.
 Yaya aka yi ya samu sunan Kaduna?
Wannan ya biyo bayan da Sardauna ya taimaka masa don ya shiga soja. Kamar yadda na kusa da Sardauna suka bayanna cewa Sardauna ba ya kyamar kowa, don haka ya taimaka masa ya shiga soja a nan Arewa inda ya sa Kaduna a cikin sunansa. Maimakon yankin da iyayensa suka fito wato Asaba. Domin Sarkin Motar Sardauna Alhaji Ali Kwarbai ya tabbatar ce Sardauna ne ya sa Nzeogwu a soja. Sannan lokacin da yake soja yana zuwa gaida Sardauna a gidansa.
 Me ya sa ake ce masa “dan Abakwa”
Bayan da ya kashe Sardauna ne aka fara yi masa wannan lakabi. Amma shi ba dan Abakwa ba ne, yana zuwa hutu ne wurin baffansa Anthony. Mutanen Abakwa ba sa son jin ana alakanta dan tawayen da wannan unguwa ta Abakwa.
 Yaya ka samu labarin kashe Sardauna?
 A ranar da aka yi tawayen ina shago, sai muka yi ta maza muka je mu ga abin da ke faruwa a gidan Sardauna. Domin mun ji cewa gidan na ci da wuta. Da muka isa gidan inda ake ta kokarin kashe gobarar, sai na wuce gidan Alhaji Isa Kaita inda ni da Alhaji Sa’idu Barda da Hajiya Ta-Funtuwa muka kwashe kayan gidan Alhaji Isa kaita zuwa gidansa na kashin kansa da ke Titin Dutse.
 Yaya labarin shi baffan Nzeogwu wato Anthony?
 Ya ci gaba da harkokinsa har zuwa lokacin da aka yi “A-raba,” kafin a fara Yakin Basasa. Domin a gidansa ’yan kabilar Ibo suka taru kafin su shiga jirgi su nufi Kudu a 1967.
 Shin mene ne tarihin Abakwa?
Abarshi tsohon soja ne da ya yi Yakin Duniya na Biyu. Shi asalinsa mutumin Zuru ne ta Jihar Kebbi, wato Badakkare ne. Shi ne ya sari garin domin da shi kadai ne a wurin. Sai aka fara ce ma wurin Abarshi daga baya ’yan kabilar Ibo da ba su iya fadin Abarshi sai dai su ce Abakwa.  An yi wa Abarshi mai unguwa har karshen rayuwarsa. Wadanda suka fara zama a unguwar su ne ma’aikatan titin jirgi. Kuma saboda tsohon gari ne, shi ya sa bai da tsarin tituna irin na zamani kamar na wasu unguwanni.
An shaida mana cewa a lokacin Yakin Basasa, sojojin Najeriya sun yi wa Manjo Chukwuma kwanton bauna suka kashe shi a garin Nsukka ranar 26 ga Yulin 1967. Kuma an dauko gawarsa aka yi mata faretin soja sannan aka binne a makabartar sojoji da ke kan titin Kashim Ibrahim a Kaduna don mutane su san cewa lallai ya mutu, bisa izinin Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon.