✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan takarar PDP ne zababben Gwamnan Bayelsa- Kotun koli

Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC ta shigar gabanta game da hukuncin kotun ranar 13 ga Fabrairu 2020, wanda ta…

Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC ta shigar gabanta game da hukuncin kotun ranar 13 ga Fabrairu 2020, wanda ta bada umarnin soke zaben dan takarar APC David Lyon tare da mataimakinsa Degi Eremionyo.

Mai shari’a Amina Augie, ta sanar da hakan sannan ta umarci lauyoyin APC da na David Lyon da manyan lauyoyi da suka hada da: Afe Babalola da Wole Olanipekun, su biya wadanda suke kara Naira miliyan 60.

Sai dai alkalin da ke jagorantar lauyoyin da suka shigar da karar Sylvester Ngwuta, ya bukaci kotun da sake yin bitar hukuncin da aka zartar a baya.