✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan ta’adda ya kashe jami’in DSS a Kuros Riba

Wani da ake zargin dan ta’adda ne ya harbe wani jami’in tsaro na farin kaya (DSS) sannan ya juya ya harbi Babban Jami’in ’Yan sandan…

Wani da ake zargin dan ta’adda ne ya harbe wani jami’in tsaro na farin kaya (DSS) sannan ya juya ya harbi Babban Jami’in ’Yan sandan yanki (DPO) kafin ya tsere.

Lamarin ya faru ne a Sankwala, Karamar Hukumar Obanlikwu da ke Jihar Kuros Riba.

Jami’in tsaron farin kaya mai suna Michael Orusede da abokan aikinsa, sun biyo dan ta’addan ne za su kama shi, inda shi kuma ya bude musu wuta.

Wani wanda ya shaida musayar wutar da aka yi a tsakaninsu, mai suna Denis Abasi ya ce, “A kokarin kwace makamin da aka gani a hannun dan ta’addan ne ya sanya shi kuma ya bude musu wuta.” Shi kuma DPO mai suna SP Effiom Okon, rauni ya samu, a sakamakon harbin da ya yi masa.

Aminiya ta tuntubi Irene Ugbo, Kakakin Hukumar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin.

Ta ce an kama wanda ake zargi da harbin jami’an, yana hannunsu kuma da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da shi a gaban shari’a.