Hankula sun tashi a yankin Fadar Shehun Borno yayin da wani jami’in dan sanda ya harbe wani sojan kasa da ke karkashin rundunar Hadin Kai, Donatus Vonkong.
Majiyoyi da dama sun tabbatar wa Aminiya a ranar Laraba cewa, dan sandan da ya aikata wannan aika-aika yana cikin maye ne bayan ya yi mankas barasa.
- Dalilin da aka dakatar da shirin ‘Idon Mikiya’
- Shari’ar Abduljabbar ta danne ta Dan Sarauniya a Kano
Bayanai sun ce wannan lamari ya tashi hankulan alumma a yankin tun bayan faruwarsa a ranar Talata, wanda hakan ya sanya mazauna yankin suka noke a gidajensu don gudun abin da ka iya zuwa ya dawo.
Sai wakilinmu ya ruwaito cewa, wasu fusatattun matasa a yankin sun sha alwashin daukar fansa kan duk wani jami’in dan sanda da suka kyallara idanunsu a kansa a yankin.
Tuni da mahukunta sojin Najeriya suka yi kira da a zauna lafiya, suna mai cewa faruwar wannan abun al’ajabi da a yanzu bincike ya kankama a kansa ba ya nufin akwai tsamin dangarkata ko wata adawa a tsakanin hukumomin tsaron biyu.
Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake yayata cewa rundunar sojin kasan Najeriya na zargin rundunar ’yan sandan kasar da cin zarafin wasu jami’anta.
Mazauna yankin da suka labarta wa wakilinmu yadda ta kasance, sun ce sojan da aka harbe shi ne ya tseratar da rayuwar Shehun Borno a wani harin kunar baki wake da aka kai a shekarar 2012.
Majiyar ta ce, “Donatus Vonkong jamii ne mai farin jini kasancewar a shekarar 2012 ya tseratar da rayuwar Shehun Borno a wani a harin bom na kunar baki wake.
“Shi ne sojan da ya yi Shehu Borno shinge da dan kunar bakin waken wanda a dalilin haka har ya samu rauni a kafarsa. Mutum ne wanda jamaa ke matukar kauna da mutuntawa a yankin.”
Aminiya ta ruwaito cewa, a Lahadin da ta gabata ce Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi, ya nada marigayi Donatus Vonkong a matsayin Zannan Fadar Shehu Borno.
Nadin mukamin Zanna, wato dai Babban Bafade a Masaurata da aka yi wa Donatus, na zuwa ne bayan an daga likafarsa a aikin soja.