✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan PDP waliyi ne, wanda ya barta jininsa ya halarta

A cikin makon jiya Kafofin yada labaran kasar nan da na waje sun dauko labarin jagoran `yan kabilar Ijaw, kuma shugaban mutanen yankin kudu maso…

A cikin makon jiya Kafofin yada labaran kasar nan da na waje sun dauko labarin jagoran `yan kabilar Ijaw, kuma shugaban mutanen yankin kudu maso kudu, wato Neja-Delta, kuma daya daga cikin tsofaffin wannan zamanin masu rura wutar kabilancinkasar nan da sunan dansu na mulkin gwamnatin tsakiya, wato Cif Edwin Clark, inda yake fallasa asirin wasu gwamnonin jihohi da walau har yanzu suna cikin jam`iyyaru ta PDP, ko kuma sun kaurace mata, amma kuma suna adawa da salon mulkin shugaban kasa Dokta Goodluk  Jonathan da dagewarsa ta lallai sai ya sake tsayawa takarar a inuwar jam`iyyar ta PDP a zabubbukan shekara mai zuwa in Allah Ya kaimu. A cikin dai makon jiyan ne a tarurruka daban-daban da dukkan masu ruwa da tsaki na jam`iyyar PDP suka gudanar, suka bada shelar sun ba Shugaba Jonathan takarar nemn shugabancin kasar nan a inuwar jam`iyyarsu, ba tare da wata hamayya ba a cikin zaben shekara mai zuwa.
Ba wancan batu na amincewa shugaban kasa ya ja ragamar jam`iyyarsa cikin zaben badin nike son in yi tsokaci akai ba ayau. Ina son makalar tawa ta mayar da hankali ne akan waccan zargi da kakkausar murya da Cif Clark ya yi ga wadancan gwamnonin jihohi, wadanda wasunsu yanzu ta bayyana karara suna neman kalubalantarsa a zabubbukan shekarar mai zuwa. Gwamnonin sun hada da Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso na Jihar Kano da Alhaji Sule Lamido na Jihar Jiigawa da Cif Rochas Okoracha na jihar Imo da tsohon gwamnan jihar Kwara yanzu kuma Sanata a Majalisar Dattawa Sanata Bukola Abubakar Saraki. Dukkan wadannan mutane hudu sun taba koma haryanzu zuwa cikin jam`iyyar PDP, tun haihuwarta.
 Cif Clark, ya zargi Gwamnan Jihar Kano Dokta Rabi`u Kwankwaso da cewa a shekarar 2003, an yi masa bincike wanda daga karshe aka fito masa da farar takarda akan ya yi sama da fadi da kudin zaizayar kasa, kuma a cewarsa har yanzu wannan batu na gaban shari`a. Amma abin tambaya shi ne Ina Cif Clark da ire-irensa na jam`iyyar PDP suke yau sama da shekaru  11, ba su fito da wannan magana ba, har a shekarar 2011, suka mara wa Gwamna Kwankwaso ya sake tsaya musu takara, ya kuma ci zabe a inuwar jam`iyyarsu, sai yanzu da Kwankwason ya barranta da jam`iyyar ya koma babbar jam`iyyar adawa ta APC, ya kuma sa Shugaba Jonathan gaba wajen yin adawa da manufofinsa da na gwamnatinsa, yanzu kuma ya ce zai nemi jam`iyyarsa ta APC ta tsayar da shi takarar neman shugabancin kasa, kana ya zama mai laifi? Yanzu ke nan tunda ya barranta da ita sai ya saurari tayar da waccan shari`a? Dama `yan jam`iyyar PDP a Jihar Kano kullum suna yi wa Gwamna Kwankwaso barazana da za a ci gaba da waccanshari`a.
A kan Gwamnan Jihar Jiigawa, Alhaji Sule Lamido, Cif Clark cewa ya yi “Wai Sule Lamido ne zai ce bai cin hanci da rashawa, ko wani abu makamancin haka, alhali shi Sule ya san bai kammala ilminsa na makarantar Sakandare ba, amma yanzu so yake ya tsaya takarar neman shugabancin kasa. Kamata ya yi Lamidon ya fito ya karyata waccan zargi,” in ji Cif Clarka. Nan ma abin tambaya shi ne manyan PDP suna ina yau shekaru kusan sha 16, (ciki kuwa har da kusan takwas da Lamido, yake mulkin jihar Jigwa a inuwar jam`iyyar PDP, wadda ita ta kakaba wa mutanen jihar shi), baya ga Ministan Harkokin kasashen Waje da ya yi a zangon farko na gwamnatin Shugaba Obasanjo 1999 zuwa 2003? Mun zuba idanu mu ga ko Cif Clark da ire-irensa masu neman ko ana ha maza, ha mata, sai shugaba Jonatahan ya sake dawowa kan karagar mulki a shekarar 2015, za su ci gaba da tada wannan magana ta Sule Lamidon ganin yanzu Sulen ya mayar da wukarsa cikin kube, ya janye takararsa, ya kuma ce zai mara wa shugaba jonathan don ya kai ga nasara.
Shi kuwa Sanata Bukola Abubakar Saraki, wanda ya jagoranci Gwamnan Jiharsa ta Kwara da sauran magoya bayansu, suka koma jam`iyyar adawa ta APC, Cif Clark cewa ya yi “Ku dubi Bukola Saraki da ya ke ta hayaniya. Ya yi amfani da sunaye barkatai wajen bude ajiya da sunaye daban-daban a Bankuna 18. Maimakon ya amsa tuhumar zargin da jami`an tsaro suka yi masa akan haka, sai kawai ya garzaya kotu yana rokon Kotun da lallai ta dakatar da `yan sanda daga bincikar wancan laifi,” in ji Cif Clark. Wani abu sai PDP, don me sai yanzu ake bankado wannan magana?
Akan Gwamnan Jihar Imo Cif Okoracha, wannna ya ja tsagin jam`iyyarsu ta APGA zuwa cikin waccan hadakar jam`iyyun adawa da suka kafa jam`iyyar APC, wanda kuma yanzu ya ce shi ma da shi za a fafata cikin neman takarar shugabancin kasar nan a badi in Allah Ya so. Cif Clark cewa ya yi “Bankunan kasar nan duk suna binsa bashi, abin da ya kai matsayin da Babban Bankin kasa ya umurci dukkan bankunan da kar wanda ya kara ba shi bashi. Amma yana hawa kan karagar mulki cikin shekara daya duk ya biya wadancan basussuka. Ina ya samo kudaden daya biya su? ” in ji Cif Clark Dattijon burgu, uban rura wutar kabilancin kasar nan a duk lokacin da ya tashi zai yi magana. Daga karshe Cif Clark ya sha alwashin ba gudu ba ja da baya Shugaba Jonathan zai tsaya zabe kuma zai ci.
Mai karatu tsarin PDP ke nan babbar jam`iyyar siyasa mafi girma a nahiyar Afirka mai ikirarin za ta yi ta mulki daga nan har shekaru  60, masu zuwa in Allah Ya kaimu. Da irin wannan kama karya za ka san cewa tsohon Gwamnan Jihar Adamawa, Alhaji Murtala Nyako da karfin tsiya PDP ta tsige shi, bisa laifin kawai ya barta ya koma jam`iyyar APC, amma ba wai don ya yi laifi ba. Shi kansa Gwamnan Jihar Nassarawa da ya sha da kyar daga hannun `yan Majalisar Jihar  na PDP kwanan baya, ai ba wani laifi ya yi ba, illa dai kawai PDP na ganin yanzu ya kamata ta gyara masa zama, ya bar gwamnati. Sauran gwamnoni irin na jihohin Kwara da Sakkwato da Kano da Ribas, sun sha ne kawai don an san ba za su tsigu ba.
A gefe daya kuma ga tsohon Gwamnan Jihar Barno, Sanata Ali Modu Sharif da aka zarga da hannun da yake da shi wajen mara wa ’yan kungiyar Boko Haram, amma tun da ya ce ya bar APC, ya dawo PDP, bayan ya zaman babban na hannun damar shugaba Jonatahan, ya kuma zama baya tabuwa. Jam`iyyar PDP ke nan da idan kana cikinta kai waliyi ne, in ka barta jininka ya halatta.