Wani dan Najeriya ya nuna bajintar cewa, shara na iya zama wani abu mai amfani da ban mamaki ta yadda ya yi wata dabarar kera kadar robobi.
Matashin ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter a @aozforum, inda ya nuna hotunan kadan yana tafiya.
- Yajin aikin Kaduna: Al’amura sun yi tsaya cik a Zariya
- An dawo wa Najeriya N2.5bn daga kudin da Ibori ya sace
Ya bayyana abubuwa uku da ya yi amfani da su wajen hada kadan da yadda ya fara har ya kammala.
A shafin @aozforum an sanya masa suna da: “Sharar gida da ake watsarwa, almubazzaranci ne don tana iya zama mai amfani!”
Sakon da ya wallafa ya janyo martani bayan irin wannan nau’o’in baje kolin abin da ya sarrafa da sharar robobin.
Sanya hotunan a shafinsa na Twitter ya sa ya samu mabiya sama da dubu 9 tare da bai wa masu bibiyar shafin mamaki saboda ganin yadda kadan ke tafiya bayan kera shi.
Wadansu kuwa martani suka yi cewa, zai yi kyau a adana kadan a harabar wasan yara.
Kafar yada labarai ta Legit.ng ta tattara wasu ra’ayoyin mabiya shafinsa na Twitter kamar haka: @skipkid20 ya rubuta: “Na zaci wannan kada na gaske ne mai rai, ba hada shi aka yi ba, amma wannan mutum ya yi bajinta kamar ya yi hauka ne?”
Shi kuwa wani a shafinsa na @ gregory_kess ya ce: “Ina son in fada maka ka yi kokari, sai da na natsu kafin na gane bayanin hotunan da ka wallafa… “Ka hadu da yin abu mai kyau!”
Shi kuwa @KStressacchi sha’awar hotunan ya yi inda ya ce: “Za a iya samun irin wannan shara a ajiye su a wuri guda, inda za a iya sarrafa sharar zuwa wasu abubuwa da za a iya nunawa.”
Shi kuwa @goduche cewa ya yi: “Da farko na zaci kadan na gaske ne, sai na yi saurin bude hotunan don ganinsu a zahirin abin da ke faruwa.”