✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Majalisar Dattawa Longjan ya rasu

Dan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar jihar Filato ta Kudu Ignatius Longjan, ya rasu. Dan majalisar na daya daga cikin ‘yan takarar APC da ya…

Dan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar jihar Filato ta Kudu Ignatius Longjan, ya rasu.

Dan majalisar na daya daga cikin ‘yan takarar APC da ya yi nasara a zaben 2019 inda ya doke abokin takararsa na jam’iyyar PDP.

A safiyar ranar Litinin ne aka samu sanarwar rasuwar Sanatan daga gidan gwamnati, inda sanarwar ta bayyana cewa  ya rasu ne bayan gajeruwar lafiya.

Dan majalisar, wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin al’adu da yawon bude ido a majalisar dattawan, ya taba zama mataimakin gwamnan jihar Filato David Jang daga shekara 2011 zuwa 2015.

Ya taba zama dan takarar Gwamnan Filato daga jam’iyyar PDP a shekarar 2015.