Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Bodinga da Dange da Shuni da Tureta na Jihar Sakkwato, Dokta Balarabe Kakale, ya ware naira miliyan 200 don rabawa Almajiran da ke mazabarsa jarin da za su samu sana’o’i domin dogaro da kawunansu.
Wata tattaunawa da aka yi da Dan Majalisar jim kadan bayan ya raba ababen hawa guda 33 da Babura guda 60 da Kekunan Dinki guda 40 da Injinan markade da dai sauransu ga rukunin farko na wadanda suka amfana da tallafin, ya ce ya yi haka ne don karkatar da tunanin Almajiran daga bara zuwa sana’o’in da za su nemi na kansu.
Dan Majalisar ya bayyana cewa za a ci gaba da wannan shirin kuma yana da kudurin samar wa kimanin Almajirai 1000 sana’o’i a wannan shekarar da muke ciki wanda a cewarsa ya ware kudin ne don tallafawa Makarantun Allo da Malamansu.
“Wannan dalilin ne ya sa muka raba kananan motocin dakon kaya guda 4 ga Makarantun Allo da raba Babura masu kafa biyu guda 33 ga Malamansu don su rika samun ’yan kudade a hannusu domin amfanin yau da kullum.”
“Kazalika, mun samarwa Alaranmomi da suka kammala Makarantun Allo da Mata da masu bukata ta musamman da sauran mutane sana’o’in da za su dogara da kansu da kuma ba su kayan aiki da rancen da ba ruwa a cikinsa,” in ji shi.
Dan Majalisar ya ce sun sanyawa shirin suna “Kowa Ya Iya Allon shi, Ya wanke” da manufar Almajirai su dogara da kawunansu.
Kakale, wanda ya goyi bayan kudurin inganta rayuwar Almajirai a zauren Majalisar Tarayya ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya na da kudurin fitar da ‘Yan Najeriya Miliyan 100 daga kangin talauci, wanda a cewarsa shirin ba zai yi nasara ba muddin ba a shigar da Almajirai a cikinsa ba.
Ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari da Ministar Kula da Ayyukan Jinkai da Gwamnatin Jihar Sakkwato bisa kokarinsu na kyautata rayuwar Almajirai a fadin kasar nan.