Baban Daraktan kamfanin gini na Asbat Construction, Temitope Banjoko, ya shiga hannun Hukumar Yaki da Almundaha (ICPC).
Wani babban jami’in ICPC da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa, Bonjoko wanda dan Kwangilar Kotin Koli ne ya shiga hannu saboda zargin sa da almundahanr kudi.
- Ba ma goyon bayan haramta mana sayar da giya – Masu wuraren shakatawa a Abuja
- China na kokarin mamaye Duniyar Wata ita kadai – Amurka
Majiyar ta bayyana cewa kamfanin ya karbi kwangilar rushewa da kwashe baraguzan gidajen wasu alkalai hudu da ke unguwar Maitama a Abuja a shekarar 2017, a kan Naira Miliyan 4,305 har da kudin haraji.
To sai dai duk da kudin sun shiga asusun kamfanin na Asbat, dan kwangilar bai aiwatar da aikin ba, wanda hakan ya sanya Kotun Kolin ta kai wa ICPC kara.
A hannu guda kuma yunkurin da muka yi na ji ta bakin Kakakin hukumar, Misis Azuka Ogugua, kan lamarin ya ci tura, kasancewa mun gaza samun ta a wayar tarho.
Karin bayani na tafe….