✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan hidimar kasa ya rasu a ruwa

A farkon wannan mako ne wani mai yi wa kasa hidima (NYSC) dan shekara 26 mai suna Joseph Adebayo, ya rasu a cikin madatsar ruwa…

A farkon wannan mako ne wani mai yi wa kasa hidima (NYSC) dan shekara 26 mai suna Joseph Adebayo, ya rasu a cikin madatsar ruwa ta Gubi da ke Jihar Bauchi, lokacin da suke yawon shakatawa domin nuna murna da kammala aikin nasu.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce, “Rundunar  ta samu rahoto daga wani mai suna Mahadi Habila Sada, wanda yake kula da ofishin shiyya na matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC), wanda ya ce an tura wadansu daga cikin masu hidimar kasa zuwa Hukumar Tara Kudin Haraji ta Jihar Bauchi, inda suka je wanka a madatsar ruwa da ke Gubi domin murnar kammala aikinsu na shekara guda. Amma sai uku daga ciki suka shiga cikin jirgin ruwa abin takaici sai jirgin ya gamu da hadarin shigowar ruwa wanda hakan ya sanya jirgin tangal-tangal ya kife, wadansu masunta ne suka ceto rayukan biyu daga cikin matasan, amma Joseph Adebayo wanda ya fito daga Jihar Ogun ya fado daga cikin jirgin ya kuma nutse hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa sai bayan kwana guda aka tsamo gawarsa.”