✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan ƙabilar Ibo ya zama Limamin Babban Masallacin Abuja

A yau sabon limamin Masallaci Abuja, ɗan ƙabilar Ibo, Farfesa Iliyasu Usman, zai fara jagorantar Sallar Juma'a a masallacin.

A karon farko ɗan ƙabilar Ibo ya zama Babban Limami a Babban Masallacin Ƙasa da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Hukumar gudanarwar Babban Masallacin ta sanar naɗa Farfesa Iliyasu Usman ɗan asalin ƙabilar Igbo daga jihar Imo a matsayin limamin juma’a.

Da naɗin sabon limamin, yanzu limaman juma’a na masallacin sun zama huɗu ke nan, ƙarƙashin jagoranchin Babba Mai Kula da masallacin, Farfesa Ahmad Shehu Galadanchi.

Manyan Limaman su ne:

  1. Farfesa Sheikh Ibrahim Maqari.
  2. Farfesa Sheikh Muhammad Kabir Adam
  3. Dakta Ahmad Onilewura
  4. Farfesa Iliyasu Usman

A yau Juma’a, 18 ga watan Oktoba, 2024 ake sa ran sabon limamin zai fara jagorantar Sallar Juma’a a masallacin.