Shugaban Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) Farfesa Umaru dambatta ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi amfani da damar da suka samu ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa irin na zamani (Intanet) da suka hada da Facebook da WatsApp da Google+ da sauransu a kan hanyar da ta dace. Ya ce ya dace a rika amfani da hanyoyin sadarwar ta hanyar baza sahihan bayanan da za su taimakawa tattalin arziki da na siyasa da na zamantakewa da kuma na ci gaban kasa.
Farfesa dambatta ya yi wannan kalami ne bayan Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar Mista Tony Ojobo ya wakilce shi a taron shekara-shekara da kafar watsa labarai ta CKN News ta shirya a kwanakin baya a Legas. An yi wa taron taken: “Gudunmawar da bangaren sadarwar zamani ke bayarwa game da ci gaban tattalin arziki da na siyasa a Najeriya.”
Ya ce duk da yake hukumarsa ba ta da ikon hana masu amfani da kafofin sadarwar zamani ta hanyar da ba ta dace ba amma akwai dokar da kafa a shgekarar 2015 don yaki da masu amfani da kafar sadarwar ba bisa ka’ida ba (Cybercrimes Act 2015). Don haka ne ya yi kira ga masu amfani da kafofin sadarwar su rika yin taka tsan-tsan wajen bin doka da oda.
Babban bako a wajen taron Ministan Sufuri Honorabul Rotimi Ameachi ya bayyana yadda wadansu ke amfani da kafofin sadarwa irin na zamani don cin mutuncin wani ko wasu ta hanyar baza bayanai da hotunan karya. Daga nan sai ya yaba wa gogaggun ’yan jaridun da suka rungumi harkar sadarwar zamani wajen gudanar da aikin jarida mai tsafa a bisa doka da oda.
Taron wanda ya samu halartar manyan bakin da suka hada da Shugaban Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa (FRSC) Dokta Boboye Oyeyemi, Farfesa dambatta ya yi kira ga hukumomi da kamfanoni masu zaman kansu da al’ummar kasa da su yi amfani da damar sayen muhimman adana bayanai (data) daga hukumarsa da hakan zai ci gaba da bunkasa tattalin arziki da na zamantakewa da na siyasa a kasar nan. Ya ce ta hanyar sayen adanannun bayanan da hukumarsa ke samarwa ne kadai za a rage masu dogaro da shafukan abota irin na zamani.
Farfesa dambatta daga nan sai ya yi alkawarin ci gaba da shirya taruruka don hada kan masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa don wayar musu da kai a kan muhimmancin bin doka da oda a game da yadda ake amfani da yanar gizo.