✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalung ga Farfesa Ango: Ka ji da jikokinka

Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung ya shawarci jagoran Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) Farfesa Ango Abdullahi kan ya kame girmansa kuma ya yi kokarin…

Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung ya shawarci jagoran Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) Farfesa Ango Abdullahi kan ya kame girmansa kuma ya yi kokarin ji da jikokinsa, maimakon bata Gwamnatin APC ta Shugaba Muhammadu Buhari.

Minista Solomon Dalung ya bayyana haka ne a martanin da ya mayar ga jagoran Kungiyar NEF lokacin da yake tattaunawa da gidan rediyon BBC a shekaranjiya Laraba

A farkon mako ne Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana cewa kungiyar ba za ta goya wa Buhari baya ba a zaben 2019 da ke tafe, bisa abin da ya kira “babu wani abin ci gaba da gawamnatinsa ta yi kusan shekaru hudu na mulkinsa.”

Yayin da yake mayar da martani a hirarsa da BBC, Minista Solomon Dalung ya ce ba irin wadannan kalaman ba ne suke bukata daga wajen dattawan ba.

“Ubangiji Ya hana su karfin fada a yanzu, Ya bar su da basira ta bayar da shawarwari da kuma dora mu a kan hanya,” inji Dalung.

Ya kara da cewa Farfesa Ango Abudllahi, a matsayin uba yake a wajensa kuma dattijo ne mai martaba kwarai a Arewa wanda ba zai tsaya yana cece-ku-ce da shi ba. “Farfesa Ango yana da jikoki, sun yi masa yawa, saboda haka bai ma san abin da ke faruwa ba a Arewa. Wannan kuskure da suka ce sun gani mu ba mu gan shi ba,” inji shi.

Ya ce kila Farfesan ya dade bai fita waje ba balle ya san halin da Arewa take ciki. “Duk wanda ya ce Buhari bai tabuka komi ba to bai masa adalci ba.”

A cikin bayanin Farfesa Ango ya ce “Buhari ya gaza magance talauci da matsalar ilimi a Arewa.”

Ya ce Arewacin Najeriya ne dandalin talauci, kuma yankin ne ya dage wajen ganin Buhari ya lashe zaben Shugaban Kasa a shekarar 2015. “Mun sa ran za a samu canji bayan Buhari ya ci zabe amma mun zuba ido ba mu ga komai ba,” in ji Farfesa Ango.

Amma a cewar Minista Dalung, Buhari ya bayar da aikin gyara hanyar Abuja zuwa Kano, gyaran da ya ce “PDP da ta yi shekara 16 ba ta yi shi ba,” inji shi.