✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dalilin sanya maballai a jikin aljifan wando jins

Abubuwan da ke jikin kayan amfani da ba a san ainihin amfaninsu ba.

Akwai abubuwan amfani birjik da ba kowa ne ya san amfaninsu ba kuma ba a fiye damuwa a san amfaninsu ba.

Idan aka lura, za a ga akwai kofa ’yar karama da ke jikin kwadon rufe kofa, da ’yar kofa da ke jikin tsinken alawa da dai sauransu.

Duka wadannan da ma wasu ana yin su ne saboda wani amfanin da ake yi da su ba wai don ado ba. Kadan daga cikin abubuwa sun hada da:

 Karamar kofa da ke jikin kwadon rufe kofa

A lokutan damina idan ana ruwan sama, ta wannan kofa ruwa kan fita idan ya shiga cikin kwado, sannan idan kwado yayi tsatsa ta wannan kofa akan zuba mai domin tsatsar ta fita.

’Yar kofar da ke jikin tsinken alawa

Wasu kan yi tunanin cewa wannan kofa an yi ta ne saboda yara su rika busa tsinken a matsayin usir, amma ba haka ba ne.

Amfanin wannan kofa shi ne, idan aka hada alawar, lokacin da ake zuba ta a jikin tsiken, kofar ke taimakawa wajen rike alawar ta bushe a jiki.

’Yar jakar kemila da ke cikin kayan waje

Wannnan kemikal da ke cikin wannan ’yar jaka yana taimakwa wajen zuke danshi, shi ya sa ake saka shi a cikin kayan waje musamman takalma da jakunkuna don kawar da danshi daga ciki.

‘Yar akwati mai kala a karshen ledar makilin

A karshen ledar man goge baki akan samu ’yar alama mai laudin shudi, baki ko kore, wanda wasu ke cewa launukan na nuna irin sinadarin da ke cikin man goge bakin ne.

Amma a hakikanin gaskiya masana’antu na sanya ana sanya alamar ce domin gane kasar ledar a yayin bugawa.

Kofar kan murfin biro

Amfanin wannan kofa shi ne barin iska ta rika fita daga cikin murfin.

Wani lokaci akan manta a sa murfin biro a baki ko kuma yara su sa a baki; wannnan kofa ke taimakawa wajen fitar da iskar da ke fita daga baki.

Dogon wuyan kwalba

Ana yin kwalba da dogon wuya ne domin samun sauki yayin da ake shan wani abu ko ake juyewa a cikin wani abu daga kwalbar.

Igiyar bayan rigar shet

Babban amfaninta shi ne sagale kaya. Dinka wannan igiyar ya samo asali ne daga sojojin ruwa, idan suna kan jirgi sukan rasa wurin ajiyar kaya, wannan ya sa suka rinka dinka yar igiyar saboda sakale kayansu.

Maballan jikin aljifan jins

Ana sa wadannan maballai ne domin hana wandon  mutuwa ko yagewa daga mahadar aljihu. Kamfanin jins na Levi Strauss ne ya kirkiro da maballan (rivets)  bayan masu hakar ma’adanai sun yi masa korafi cewa jins dinsu ke mutuwa ta matar aljihu a shekarar 1829.

Wannan yar kibiya na nuna kofar tankin mota, idan ta kalli hagu to kuwa murfin na daga barin hagu haka ma hannun dama.