Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ainihin dalilin da ya sa ya ki amfani da shawarar da Bankin ba da Lamuni na Duniya (IMF) da sauran masana tattalin arziki suka ba shi kan cire tallafin man fetur.
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da jaridar Bloomberg.
- Kiristoci masu ziyarar ibada daga Najeriya sun isa Jordan
- An sace mahaifiyar dan takarar Sanatan APC a Jigawa
Ya ce dole ta sa yanzu hatta kasashen Yamma sun fara fahimtar banbancin abin da yake a takarda da kuma na zahiri.
Da aka tambaye shi dalilin kin cire tallafin, Buhari ya ce, “Yawancin kasashen Yamma yanzu suna biyan tallafin man fetur. Mu ban ga dalilin da zai sa mu cire namu ba. In kura na maganin zawo me zai hana ta yi wa kanta?
“Da farko gwamnatina ta shirya cire tallafin gaba daya nan da karshen shekarar nan. Amma bayan doguwar tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma la’akari da abubuwan da ke faruwa, mun fahimci hakan ba zai yiwu ba.
“Abin da muka fi bukata shi ne inganta yawan man da muke hakowa da kuma tacewa. Yanzu haka muna hada gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu na Dangote da BUA da kuma Waltersmith wadanda suke kafa matatun mai.
Da zarar mun kammala kafa wadannan masana’antun na bangaren mai da kuma na samar da abinci, matsalar hauhawar farashin kayayyaki za ta kau a Najeriya,” inji Buhari.
A baya dai IMF da Bankin Duniya da masana tattalin arziki da dama sun sha ba Shugaban shawarar janye tallafin gaba daya.