✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa na rina gashina – Lionel Messi

Shahararren dan kwallon kulob din FC Barcelona Lionel Messi ya fito fili ya bayyana dalilinsa na rina gashinsa zuwa fari maimakon baki a kakar wasa…

Shahararren dan kwallon kulob din FC Barcelona Lionel Messi ya fito fili ya bayyana dalilinsa na rina gashinsa zuwa fari maimakon baki a kakar wasa ta bana.
Lionel Messi, wanda a da gashin kansa baki ne, masoya kwallon kafa sun wayigari ya canja gashi ne bayan da aka fara kakar wasa ta bana, musamman gasar La-Liga ta Sifen.
Messi ya ce ya yanke shawarar rina gashinsa ne domin ya huce takaicin yadda kasar Ajentina ta rasa damar lashe Kofin Nahiyar Kudancin Amurka da aka fi sani da Copa-America a karo biyu a jere bayan kasar Chile ta yi mata kafar ungulu sai biyu a jere kuma a wasan karshe.
Hakan ta sa Messi ya bayyana yin ritaya daga yi wa kasarsa wasa amma daga baya aka shawo kansa ya canja shawara inda yanzu haka ya ci gaba da buga wa kasar tasa kwallo.
“Saboda takaicin yadda kasar Chile ta doke Ajentina sau biyu a jere a wasan karshe na Copa-America ne ya sa na rina gashina don na fita daga takaici,” inji Messi.
Masoya harkar kwallo musamman magoya bayan kulob din FC Barcelona sun yi mamakin yadda Lionel Messi ya canja launin gashinsa zuwa fari bayan da aka fara kakar wasa ta bana al’amarin da ta sa da yawa daga ciki ba su san dalilinsa na yin haka ba sai yanzu da ya fito fili ya yi bayani.
Shi ma takwaransa dan kasar Brazil Neymar an ga ya kwaikwayi Messi wajen canja launin gashinsa zuwa fari al’amarin da ya sa ake hasashen watakila shi ma Luis Suarez zai bi sahu wajen canja launin gashinsa zuwa fari domin su yi anko.