✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa na bar qwallo a Oman na dawo Najeriya – Umar Martaba

Aminiya ta samu zantawa da wani matashin dan wasan kwallon kafa mai suna Umar Martaba, wanda duk da cewa matashin dan wasa ne, amma ya…

Umar MartabaAminiya ta samu zantawa da wani matashin dan wasan kwallon kafa mai suna Umar Martaba, wanda duk da cewa matashin dan wasa ne, amma ya buga kwallo a kasashen waje, sannan kuma ya dawo gida Najeriya inda ya ci gaba da buga kwallon da burin nan gaba kadan zai sake komawa kasar waje domin ya ci gaba da wasa. A tattaunawar, ya shaida wa Aminiya cewa babban burinsa shi ne ya haskaka a duniya inda ’yan uwa da abokan arziki za su gan shi kuma su yi alfahari da shi. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya : Ka gabatar da kanka ga masu karatu?
Martaba: Sunana Umar Martaba. An haifeni ne a Unguwar Kawo da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Jihar Kaduna. Na fara kwallon kafa a kungiyar S.A.D Kawo, to a nan nake ta buga kwallo har Allah Ya sa muka fara zuwa jiha-jiha muna buga kwallon kafa, daga nan sai Allah Ya daga ni har je kungiyar Jigawa Golden Stars, a nan ne na fara buga babbar kungiya a nan Najeriya, daga nan sai na koma Ajiya Babes da ke Gumel inda muka dago kungiyar har zuwa rukuni na biyu, daga nan sai na tafi kasar waje inda na fara da wata kungiyar da ake kira FC Gagra da ke kasar Georgia inda na yi shekaru biyu zuwa uku, daga nan sai na koma kungiyar Sama’il da ke kasar Oman inda a nan ma na yi shekara daya, daga nan kuma sai na dawo gida Najeriya inda na sa hannu a kwantiragi da kungiyar Remo Stars da ke Jihar Ogun a bara a lokacin suna buga rukuni na biyu ne, sai Allah Ya taimakemu muka dago kungiyar zuwa rukuni na daya na gasar rukunin firimiya inda muke yin wasa a halin yanzu.
Aminiya: Mene ne bambanci tsakanin kwallo a kasashen waje da kuma a nan gida Najeriya?
Martaba: Gaskiya akwai bambanci sosai, saboda ko tsare-tsarensu akwai bambanci da namu, ko filaye ma kadai idan ka lura za ka ga akwai bambanci sosai domin nasu sun fi kyau. Kuma gaskiya sun fi mu samun ci gaba a harkar kwallo. Amma yadda nake ganin ci gaban da ake samu yanzu a a gasar firimiya ta Najeriya nan da shekara biyu masu zuwa, gasar za ta iya gogayya da takwarorinta na duniya domin gaskiya an samu ci gaba sosai yanzu
Aminiya: Menene burinka a wannan harkar?
Martaba: Burin duk wani dan kwallo shi ne a san shi a duniya, a rika nuna shi a akwatin talabijin (TB), inda duk ‘yan uwa da abokanan arziki za su gan shi su yi alfahari da shi, don haka babban burina a wannan harkar shi ne in kai wani mataki inda duk iyaye da abokanan arziki za su ganni su yi alfahari dani, ma’ana in samu kungiya babba a kasar waje.
Aminiya: ko kana da burin buga wa Najeriya a nan gaba?
Martaba: Insha Allah wannnan shin e na daya ma, burin duk wani kwallo ya buga wa kasarsa, a ganina duk wanda bai buga wa kasarsa ba to gaskiya bai cika ba, da sauranshi gaskiya, don gaskiya ba karamin abu ba ne ac e yau ga shi za ka wakilci kasarka, wannan abun murna ne. Don haka ina da burin in buga wa Najeriya kwallo, kuma in Allah Ya yarda zan buga mata nan gaba.
Aminiya: Me ya sa ka baro kasar waje ka dawo gida Najeriya da wasa?
Martaba: Ka san wani lokacin a kan samu matsala tsakanin wakilinka da kungiyar da kake bugawa kwallo, wani lokacin kuma za ka iya gama kwantaraginka, amma kuma ba a sabunta maka ba, kamar a Georgia, gaskiya ni ban san asalin abun da ya faru ba, amma na san an samu matsala da wakilina da kungiyar ta FC Gagra a kan kudi, saboda yana ganin ya samu wata kungiya a kasar Oman inda yake ganin zai kai ni, daga nan sai ya kai ni can kasar Oman din inda na sa hannu a kwantaragi na shekara daya, bayan kuma na buga musu na shekata daya ina da niyyar sabuntawa, sai kungiyar ta yi canjin mahukunta wanda hakan ya sa ban koma ba.
Aminiya: Menene shawararka ga matasan ’yan kwallo?
Martaba: Gaskiya yanzu samun ci gaba a kwallo bai da wahala kamar da saboda akwai dama da yawa ba kamar da ba, kuma ka ga kwallon nan fa aiki ne sosai, don haka ni shawarata ga kananan yara masu tasowa, kuma suke da burin buga kwallo ita ce su yi abin da gaske idan har sun samu goyon baya a kan su ci gaba da sana’ar, domin idan mutum ya dage, Allah Zai taimakesa. Kuma tunda suna kallo a akwatin talabijin (TB), su ma sai su dage kuma su sa Allah a gaba.
Aminiya: Mecece shawararka ga hukumar kula da wasannin firimiya ta Najeriya (LMC)?
Martaba: Gaskiya ni dai daga abun da na gani, na gamsu da kokarin da suke yi, don gaskiya ina jin dadin wasannin firimiya, kuma suna yin kokari sosai, ka ga yanzu ana zuwa gidanka a ci ka, ko a yi kunnen doki, ka ga wannan ai ci gaba ne. Ko a makon da ya gabata mun yi kunnen doki a waje, kuma mu ma mun yi kunnen doki biyu a gida, don haka ba laifi gaskiya, sai dai kawai a kara duba wasu abubuwa a kara gyara su.
Aminiya: Ya yanayin kokarinku a kakar wasa ta bana?
Martaba: Gaskiya ba kamar yadda muka so ba, amma mun gode wa Allah, ba wai bai yi daidai ba ne, ko kuma mun gaza, amma kawai sa’a ce ba mu samu ba saboda gaskiya muna kokari sosai kuma muna kara kwazo domin mu ga mun gyara wadansu kura-kurai, amma muna rokon Allah Ya ba mu sa’a a wasanninmu na gaba.
Aminiya: Menene kiranka ga masoyanku?
Martaba: Su kara hakuri, kuma muna godiya saboda ka ga ba ma ba su abin da suke so, don haka ne muke kara lallabarsu, kuma gaskiya muna godiya da yadda suke tare da mu a kodayaushe.