✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa Hawainiya ke sauya launin jikinta

Masana sun ce harshen hawainiya ya yi tsayin jikinta sau biyu ko uku. Hakan ta faru ne saboda harshen na taimaka musu wajen farautar kwarin…

Masana kimiyyar dabbobi na na ra’ayin cewa, hawainiya na daga cikin dabbobi masu matukar ban sha’awa da rashin zafin nama a doron kasa.

Hawainiya dabba ce mai siffofi na musamman, kama daga yanayin idanunta, yanayin harshenta, zuwa yanayin wutsiyarta da yatsunta, da baiwar iya sauya launin jikinta da dai sauransu.

Bincike ya nuna ana da nau’in hawainiya sama da 200 a duniya, kuma an fi samunsu ne a yankin Afirka, musamman kuma Madagascar.

Domin kuwa, masana sun ce rabin adadin hawainiya da ake da su a duniya, a Madagascar suke da zama.

Sannan suna daga cikin dadaddun dabbobin da aka gano suna rayuwa a doron kasa kimanin shekaru miliyan 60 da suka gabata.

Galibi, kananan kwari su ne abincin hawainiya, sai dai wasu lokuta sukan ci wasu abubuwa daban don dorewar rayuwa.

An ce hawainiya na daga cikin dabbobin da suka gabaci dan Adam zama a doron kasa, hakan ne ma ta sa ake iya samun bayanan da suka dangacesu ada ne cikin dadaddun litattafan da duniya ke ji da su.

Suna da baiwar canza launin jikinsu zuwa launuka daban-daban. Galibin launukan da suka fi canzawa su ne; shudi da ja da kore da kuma ruwan dorawa.

Dalilan da kan sanya su canza launin jikinsu lokaci-lokaci sun hada da; badda kama don kauce wa cutarwar manyan kwarin daji da mutane, wata alama ce ta sadarwa a tsakaninsu da dai sauransu.

A cewar masana, harshen hawainiya ya yi tsayin jikinta sau biyu ko uku. Hakan ta faru ne saboda harshen na taimaka musu wajen farautar kwarin da suke ciki.

Sun ce, hawainiya ba su da kaifin ganin wuri daga nesa sai in sun matso dab da abu, wannan ya sa harshen nasu ke taimaka musu wajen kama duk karamin kwaron da suka gani daga nesa a matsayin abinci.